Najeriya, kasa mafi yawan al'umma a Afirka, kuma babbar abokiyar kawancen kasashen yammacin duniya a yakin da ake yi da masu tada kayar baya a Afirka ta Yamma, ta yi aiki ba tare da jakadu ba tun watan Satumban 2023.
A baya dai ministan harkokin wajen kasar ya dora laifin rashin kudi a kan jinkirin nada sabbin jami'an diflomasiyya.
Wata majiyar gwamnati ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa "ana kan warware matsalar" kuma wannan na nufinm "nan ba da jimawa ba za a sanar da nadin."
Jami’an tsaron Najeriya na gudanar da binciken kwakwaf kan mutanen da mai yiyuwa a nada a mukaman, kuma sun fara bayyana sakamakon bincikensu ga hukumomin da abin ya shafa, a fadar shugaban kasa da na majalisar dokoki, kamar yadda wani jami’in leken asirin ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Mai magana da yawun fadar Shugaban kasar ya mika tambayoyin ga ma’aikatar harkokin wajen kasar wadda ba ta bada amsa ba. Majiyar ta ki bayyana sunayensu saboda ba su da izinin yin magana kan lamarin.
Dandalin Mu Tattauna