Gwamnatin jihar Filato ta sake ayyana dokar hana yawo ta tsawon sa'o'i ashirin da hudu a karamar hukumar Mangu, biyo bayan sake barkewar wani rikici da yayi sanadin rasa rayuka da kone-konen gidaje.
Shugaban riko na karamar hukumar Mangu a jihar Filato Markus Artu, ya ce sun dakatar da duk zirga-zirgar motoci da babura in ban da jami’an tsaro da wadanda ke ayyuka na musamman.
Majalisar dokokin Jihar Nasarawa a Najeriya ta shiga rudani bayan da aka samu rarrabuwa a majalisar, lamarin da ya sa bangarorin majalisar biyu suka yi zaben kakakin majalisa a lokuta dabam dabam.
Shugabannin kananan hukumomi goma sha bakwai da daukacin kansilolin jihar Filato sun kalubalanci matakin da gwamnatin jihar ta bi, na dakatar da su daga mukamansu.
Gwamna Caleb Mutfwang ya ce "dole ne mu karya wannan yanayi na kiyayya da hare-hare, mu daina barin mutane suna mana kallon banza, don ba haka muke ba.
Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong a wani taro da shugabannan jami’an tsaro a jihar, don sake duba matakan tsaro a karamar hukumar Mangu, ya ce, sun fahinci cewa akwai wadanda aka chapke da zargin hannu a rikicin.
Hukumomi a karamar hukumar Mangu a Jahar Filato sun sanya dokar hana yawo na sa'o'i 24, biyo bayan rikicin da yayi sanadin rasa rayuka da kona dukiyoyi a yankuna da dama.
Rundunar sojin Najeriya ta sha alwashin kara dankon dangantakarta da farar hula don fahimtar aiyukanta da samar da zaman lafiya a kasa.
Kusan makonni uku kenan tun bayan da wani rikici tsakanin manoma da makiyaya ya yi sanadin rasa rayuka da kone-konen gidaje, yayin da mutanen kauyukan da ke kewaye da garin na Tattara suka yi gudun hijira zuwa garin Garaku, shalkwatar karamar hukumar Kokona a jihar Nasarawa.
Al’ummomin kauyen Tattara da sauran kauyukan da rikici ya daidaita a karamar hukumar Kokona a Jahar Nasarawa sun bukaci gwamnati ta samar musu da tsaro don su koma yankunansu su yi noma.
Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta tabbatar da mutuwar mutane goma a wani hatsarin tankar man fetur a mahadar hanyar Bauchi, dake nan cikin garin Jos.
Sama da mako guda kenan rikice-rikice ke ta kunno kai a kananan hukumomin Mangu, Barikin Ladi, Bokkos da Riyom, lamarin da yayi sanadin rayukan gomman mutane, bacewar dabbobi da kone-konen gidaje.
Rundunar ‘yan sandan Jahar Nasarawa a arewacin Najeriya ta yi nasarar kama mutane goma sha bakwai da ake zargi da ayukan garkuwa da mutane don karbar kudin fansa.
Mutane akalla tara sun rasa rayukansu biyo bayan wani rikici da ya barke tsakanin makiyaya da mutanen kauyukan yankin Tattara a karamar hukumar Kokona a jihar Nasarawa.
Wannan umurnin na zuwa ne bayan zanga-zangar da wasu mata suka kwashe mako guda suna gudanarwa don nuna rashin gamsuwarsu da sakamakon zaben gwamna a jihar, wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta ayyana gwamna mai ci Injiniya Abdullahi Sule na APC, a matsayin wanda ya lashe zaben.
Kwanaki kalilan kafin zabubbukan gwamnoni da ‘yan majalisun dokoki a wassu jihohin Najeriya, an fara samun zafafan kalamai daga wassu jama’a, wanda idan ba’a dakile su ba, za su iya janyo tashin hankali a tsakanin al’umma.
Kwanaki kalilan kafin zaben gwamnoni da ‘yan Majalisun Dokoki a wasu jihohin Najeriya, an fara samun zafafan kalamai wadanda masan ke ganin idan ba’a dakile su ba, za su iya janyo tashin hankali a tsakanin al’umma.
Rahotanni daga Jahar Binuwai na nuni da cewa mutane kimanin hamsin ne ‘yan bindiga suka hallaka a wassu kauyuka fiye da goma sha biyu, a karamar hukumar Kwande, dake Jahar Binuwai.
Zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka kammala a wannan shekarar ta 2023 ya hadu da tarin matsaloli da ke neman gyara kafin zaben gwamnoni da ‘yan majalisun dokoki.
Farfesa Shehu Abdulrahman wanda ya sanar da sakamakon ya bayyana cewa jami’iyyar Leba ce ke kan gaba da kuri’u dubu dari hudu da sittin da shida da dari biyu da saba’in da biyu.
Domin Kari