Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FILATO: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Kama Wasu Masu Garkuwa Da Mutane 26


Masu garkuwa da mutane da makamai
Masu garkuwa da mutane da makamai

Rundunar ‘yan sandan Jahar Filato ta gabatar wa manema labarai mutane 26 da ta ke tuhuma da aikata manyan laifuka daban daban.

Wadanda rundunar ‘yan sandan ta cafke sun hada da wadanda take zargi da kisan kai, yin garkuwa da mutane, mallakar bindigogi da makamai ba bisa ka’ida ba, da sauransu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jahar Filato, DSP Alfred Alabo ya ce sun kama wadanda suka yi garkuwa da daliban jami’ar Jos su bakwai, da wata mace da ta sace diyar makwabciyarta zuwa Lagos, masu satar manyan wayoyin wutar lantarki da sauransu.

Kudade da aka karbe daga hanun masu garkuwa da mutane
Kudade da aka karbe daga hanun masu garkuwa da mutane

Jahar Filato, kamar sauran jihohin Najeriya ta na fuskantar barazanar tsaro saboda yawaitar masu aikata laifi dake dankare a sassa daban-daban na Jahar.

Usman Yahaya ya ce an kama shi ne da wasu ‘yan’uwansa da laifin aikata garkuwa da wani mutum a Jahar Enugu, makwanni biyu da suka gabata, suka karbi kudin fansa naira miliyan hudu da dubu dari biyar.

Ita ma Patience Solomon an kama ta ne da sace diyar makwabciyarta ta mai watanni goma, ta tafi da ita Jahar Lagos, ta bayyana cewa ta dauke yarinyar ne don ta na son ta.

Bindigogi
Bindigogi

Shi ko Salisu Yahaya wanda ake zarginsa da yin yin garkuwa da daliban jami'ar Jos su bakwai, yana cikin wadanda suka fasa gidan gyara hali na Jos suka gudu a shekara ta dubu biyu da ishirin, ya shaida cewa abokinsa da suka hadu a gidan yari, shi ne ya yi garkuwa da daliban.

Wani dattijo mai suna Barnabas Yakubu ya bayyana cewa shi da wasu mutane sun kashe wani mutum ne a kauyensu, saboda a cewarsa, baya mutunta su.

Rundunar ‘yan sandan dai ta sha alwashin bankado duk batagari da ke boye a fadin Jahar don tabbatar da zaman lafiyar al’umma da dukiyoyinsu.

Jahar Filato ta gabatar wa manema labarai mutane 26 da ta ke tuhuma da aikata manyan laifuka daban-daban.

Wadanda rundunar ‘yan sandan ta cafke sun hada da wadanda take zargi da kisan kai, yin garkuwa da mutane, mallakar bindigogi da makamai ba bisa ka’ida ba, da sauransu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jahar Filato, DSP Alfred Alabo ya ce sun kama wadanda suka yi garkuwa da daliban jami’ar Jos su bakwai, da wata mace da ta sace diyar makwabciyarta zuwa Lagos, masu satar mayan wayoyin wutar lantarki da sauransu.

Rundunar ‘yan sandan dai ta sha alwashin bankado duk batagari da ke boye a fadin Jahar don tabbatar da zaman lafiyar al’umma da dukiyoyinsu.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG