PLATEAU, NIGERIA -Ranar 12 ga watan Agustan kowace shekara ne Majalisar Dinkin Duniya ta ware don karfafa wa matasa gwiwa ta yadda za su kara azama wajen gudanar da ayyukan ci gaban kasa da yin nazari kan matsaloli da suka zame tarnaki ga ci gaban matasan.
Kwamishinan Harkokin Matasa da wasanni a jihar Filato, Bashir Lawandi Datti, ya ce matasa su ne ginshikin zaman lafiya da ci gaban al’umma don haka ne ma suka samar da tsare-tsare domin taimakawa wajen samar musu da ayyukan yi.
Komared Emmanuel Jukun, mataimakin Shugaban Majalisar Matasan ta jihar Filato ya ce bikin matasan na bana zai karkata ne kan kare muhalli, inda shi kuma Komared Adam Khalid Muhammad ya shawarci ‘yan uwansa matasa ne da su rungumi akidar zaman lafiya.
Sai dai bikin na bana ya zo ne a daidai lokacin da jihar Filato ke fama da matsalar tsaro.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da kisan mutane 20 a wani hari cikin dare da ‘yan bindiga suka kai kauyukan Tagwam Lawuru da Layowok a yankin Heipang da ke karamar hukumar Barkin Ladi.
Rundunar ta ce mutane da dama ne suka samu raunukan harbin bindiga, ta kuma kara da cewa ‘yan sanda sun kai dauki an kuma samu kwanciyar hankali yanzu.
Harin ya zo ne kwanaki kadan bayan kisan daya daga cikin matafiya da suka fito daga kasuwar shanu a garin Bukur.
A halin da ake ciki dai lamura sun kwanta a yankin da aka kai hare-haren.
Saurari cikakken rahoto daga Zainab Babaji:
Dandalin Mu Tattauna