Shugaban kungiyar matasan kabilar Birom, Barista Solomon Dalyop, yace ko a ranar Talata an kashe mutane shida a kauyen Farin Lamba.
Shi ma shugaban kungiyar Myetti Allah a jihar Filato, Alhaji Nura Muhammad ya bayyana cewa basa jin dadin abinda ke faruwa.
Kwamishinan yada labarai da sadarwa a jihar Filato, Mr. Dan Manjang ya bukaci al’ummar yankunan su kai zuciya nesa.
A halin da ake ciki, kwamishinan 'yan sandan jihar Filato Bartholomew Onyeka, ya ziyarci al'ummar Farin Lamba ranar Laraba tare da kwamandan rundunar Civil Defense domin jajanta wa al'ummar yankin kan kashe-kashen da aka yi a yankin.
Kwamishinan 'yan sandan ya kuma tabbatar wa al’umma cewa rundunar ta tanadi duk wasu hanyoyi da suka dace don ganin an hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aikar.
Ya kuma bukaci jama’a su yi hakuri su guji daukar doka a hannunsu, su bude hanya don bada damar zirga-zirgar ababen hawa, saboda gwamnatin jihar da rundunar ‘yan sanda suna yin duk abinda ya dace don ganin an yi adalci.
Mazauna yankin sun yaba da kokarin rundunar tare da yin alkawarin kwantar da hankali.
Saurari rahoton Zainab Babaji: