Ministocin, wadanda shugaban kasar ya zabo daga jihohi, su ne za su bada shawarwari da nemo sabbin fasaha na habaka tattalin arzikin kasa, samar da tsaro, kiwon lafiya mai inganci, samar wa da kuma farfado da masana'antu, samar da ayyukan yi da sauran fannonin bunkasa kasa, ta yadda Najeriya za ta kara da sauran kasashen duniya da suka yi fice.
Sakataren kungiyar da ke fafutukar samar da sauyi mai inganci a shiyyar Arewa ta tsakiyar Najeriya wato North Central Renaissance Movement, Aliyu Mustapha Danladi ya ce dole ne shugabannin su fuskanci al'kiblar da za ta fidda 'yan Najeriya daga hali mara dadi da suka tsinci kansu a ciki.
Mr Emmanuel John Fyaktu, ma'aikaci a jami'ar Jos, ya shawarci ministocin da sauran shugabanni da su yi mulki da tsoron Allah ba tare da nuna sonkai ba.
'Yan Najeriya wadanda duk wadannan tanade-tanaden dominsu ake yi, sun bayyana cewa amana ce aka bai wa shugabannin don haka su yi kokarin hada kan 'yan Kudu da Arewa da Gabas da Yamma.
Mr. Bulus Kamshwe ya ce yana fatan a samar wa matasa ayyukan yi, amma bisa cancanta.
Ita ma Maimuna Abdullahi ta yi fatan ministocin za su bada fifiko a bangarorin dake ci musu tuwo a kwarya.
Duk da shike dukkan ministocin mutane ne kwararru a fannonin aikinsu, wasu da dama daga cikinsu sun yi rawar gani a ayyukan ci gaban al'umma, sai dai manazarta na ci gaba da tattaunawa kan wadanda suke ganin shugaban kasar ya zabo su ne don ya saka musu kan aiki da suka yi a lokacin zabe.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna