Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ayyana Dokar Hana Yawo Sakamakon Wata Tarzoma Da Ta Tashi A Karamar Hukumar Mangu, Jihar Filato


Gwamnatin Jihar Filato
Gwamnatin Jihar Filato

Gwamnatin jihar Filato ta sake ayyana dokar hana yawo ta tsawon sa'o'i ashirin da hudu a karamar hukumar Mangu, biyo bayan sake barkewar wani rikici da yayi sanadin rasa rayuka da kone-konen gidaje.

PLATEAU, NIGERIA - Rikicin ya faro ne da hare-hare da ‘yan bindiga ke kai wa kan mutane a kauyuka, wanda daga bisani ya rikide zuwa na kai hari da ramuwar gayya tsakanin al’ummomin yankin da a baya ke zaman lafiya da juna.

Shugaban riko na karamar hukumar Mangu Hon. Markus Artu, ya ce harin na baya-bayan nan ya yi sanadin rasa rayuka, a saboda haka aka sanya dokar hana fita da shiga garin na Mangu.

Wannan doka ta hana yawo a karamar hukumar Mangu ita ce karo na biyu a kasa da wata guda.

Jami’in kungiyar da ke wanzar da zaman lafiya ta kasa da kasa, wato Mercy Corp, Mr. Godwin Okoko ya shawarci al’ummar yankin da su yi hakuri da juna.

Shi ma Malam Abdullahi Gambo dake aiki a kungiyar da ke sasanta tsakanin makiyaya da manoma mai suna Pastoral Resolve, ya ce ya kamata jama’a su lura cewa wasu marasa son zaman lafiya dake amfana da rikicin ne ke tunzura mutane.

Bayanai na nuni da cewa fiye da mutane dari biyu ne suka rasa ransu a hare-haren da ‘yan bindigar suka kai kan al’ummar yankin a kauyuka da rugage fiye da hamsin, a cikin wata guda.

Saurari cikakken rahoto daga Zainab Babaji:

An Ayyana Dokar Hana Yawo Sakamakon Wata Tarzoma Da Ta Tashi A Karamar Hukumar Mangu, Jihar Filato
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG