Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Muka Yi Zanga-zanga - Daliban Jami’ar Jos


Wasu masu zanga-zanga
Wasu masu zanga-zanga

Wasu daliban jami’ar Jos sun gudanar da zanga-zangar gargadi cikin lumana, inda suka bukaci hukumomin jami’ar su rage kudin makaranta da kuma bukatar ganawa da shugaban jami’ar don bayyana masa bukatunsu.

Daliban sun yi ta wakoki suna cewa ‘’kudin makaranta ya yi yawa, ba za mu yarda ba’’.

Wani mai suna Kungmi Dogara ya ce ba za su iya biyan kudin makaranta da yanzu haka ya zarce naira dubu 160.

Ita ma Nenrit Ayuba ta ce daman daliban su ne ke biyan kudin makaranta da kansu don haka take ganin kudin ya yi yawa.

Yayin da daliban ke zanga-zanga wani uba wanda dansa ke karatu a jami’ar ta Jos, Ibrahim Maidangi, ya ce kamata ya yi hukumomi su shiga lamarin don samun rangwame.

Wasu masu zanga-zanga
Wasu masu zanga-zanga

A bangaren hukumomin jami'ar kuwa, mataimakin magatakardar jami’ar Jos a bangaren sadarwa da wallafe-wallafe, Abdullahi Abdullahi, ya bayyana cewa duk da yake daliban na da hurumin yin zanga-zanga kan abin da bai yi musu dadi ba, kamata ya yi su sani cewa al’amura sun sauya.

Abdullahi Abdullahi ya ce a kowanne wata jami’ar na kashe a akalla naira miliyan30 kan ababen more rayuwa kamar su ruwa, wutar lantarki da sauransu.

Ya kara da cewa kusan shekara guda kenan, jami’ar bata iya biyan wadanda ke share harabar jami’ar ba saboda babu isassun kudade.

Abdullahi ya ce sau uku, jami’ar na rage kudin makarantar, tun daga naira dubu 260 zuwa naira dubu 95, bisa ga fannin da dalibi ke karatu.

Ya karkare da cewa tilas ne daliban su yi sadaukarwa kamar yadda suka ci gajiyar sadaukarwa da wasu suka yi a baya, muddin ba su so a rufe jami’ar.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG