Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FILATO:‘Yan Bindiga Sun Jikkata Mutane Da Dama A Wani Sabon Hari


Jana'izar wasu da aka kashe
Jana'izar wasu da aka kashe

Hukumomi a karamar hukumar Mangu a Jahar Filato sun sanya dokar hana yawo na sa'o'i 24, biyo bayan rikicin da yayi sanadin rasa rayuka da kona dukiyoyi a yankuna da dama.

Wata sanarwa daga shugaban karamar hukumar Mangu, Mr. Minista Daput ta ce daukar matakin ya biyo bayan wani hari da aka kai kan kauyukan Kubat da Fungzai wanda ya janyo asarar rayuka da dukiyoyi.

Kansila mai wakiltar yankin, Plangji Mwesh yace a lokacin da ya ke magana, rikicin ya bazu zuwa kauyuka da dama don haka basu da adadin wadanda suka hallaka.

Jana'izar wasu da aka kashe
Jana'izar wasu da aka kashe

Shugaban matasan Bwai, Dafet Clifford yace ya ga gawarwaki hamsin da daya.

A gefe guda kuma, shugaban kungiyar Miyetti Allah a karamar hukumar Mangu, Yahaya Bello Shanono yace an hallaka mutanensa da dabbobi dama, wadansu na can suna neman agaji.

Tuni da gwamnan Jahar Filato, Simon Lalong ta bakin hadiminsa, Makut Simon Macham ya fitar da sanarwar umurtar jami’an tsaro su gagguta kamo wadanda suka aikata kisan don hukunta su.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto hukumomin tsaro ba su fidda wata sanarwa kan batun ba.

Saurari rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG