Jami’in dake aiki da kungiyar Mercy Corps dake wanzad da zaman lafiya, Mr Godwin Okoko yace ‘yan jarida na kan gaba wajen yaki da rikice-rikicen da ke aukuwa a Najeriya, don haka suka tallafa wa ‘yan jarida na Jahar Filato kafa wata kungiya da zasu taimaka wajen yayata labaran da zasu kawo hada kan jama’a.
Taron horarwar wanda ya janyo ‘yan jarida dake aikin wanzar da zaman lafiya a Jahar Kaduna, sun ba juna shawarwari kan yadda zasu gudanar da ayyukansu bisa ka’ida.
Ibrahima Yakubu, wakilin Radiyo DW ta kasar Jamus a Kaduna yace taron bitar na da tasiri wajen inganta aikin jarida, musamman a bangaren zaman lafiya.
Mr Josiah Buzun, wakilin Rediyo Najeriya yace taron bitar ya kara fadakar da shi yadda zai yi rahoto ba tare da ya tada hankalin jama'a ba.
Malam Adamu Baba dake aiki da kungiyar dake sasanta tsakanin addinai, yace taron ya bashi damar fahintar yadda zai yi aiki da ‘yan jarida wajen hana aukuwar tashin hankali tun daga matakin unguwanni.
Bayan kammala taron bitar an kuma kaddamar da kungiya ta ‘yan jarida da za ta taimaka wajen yada sahihan labarai da zasu hada kan kasa.
Saurari rahoton a sauti:
Dandalin Mu Tattauna