NIAMEY, NIGER - Suna zarginsa da shirin shiga Najeriya ta bangaren birnin Kebbi da gamin bakin wata babbar kasar da ba a bayyana sunanta ba a wannan sanarwa.
Tuni alkali mai shigar da kara ya kaddamar da bincike a cewar sanarwar ta sojojin CNSP.
Sanarwar wacce kakakin majalisar CNSP, Kanar Manjo Amadou Abdourahamane, ya karanta a gidan Talbijan RTN mallakar gwamnati a wajehen karfe 11 na daren jiya Alhamis ta zo a wani lokacin da ‘yan Nijar suka matsu su ji zahirin abubuwan da suka wakana a tsakanin fadar shugaban kasar Nijar da na unguwar Tchangaray da ke kwaryar birnin Yamai inda aka wayi gari da karar bindigogi.
Ya ce a wajejen karfe 3 na daren Laraba wayewar Alhamis hambararren Shugaban kasa Mohamed Bazoum da iyalinsa da ke samun rakiyar masu dafa masa abinci su biyu da wasu jami’an tsaro biyu ya yi yunkurin tserewa daga inda ake tsare da shi.
Yunkurin wanda bai yi nasara ba ana hasashen an kitsa shi akan tsarin da ke nunin wata mota na jiransu a kewayen fadar shugaban kasa don kai su inda aka yi mahada wato wani allon tallace-tallace da ke unguwar Tchangaray ta bangaren arewacin birnin Yamai.
Daga nan kuma an tsara ficewa da su zuwa wani wuri inda jirage biyu masu saukar angulu mallakar wata babbar kasa ke jiransu don kai su birnin Kebbi a tarayyar Najeriya.
Sai dai jajircewar jami’an tsaro ta ba da damar dakile wannan yunkuri na tayar da hankalin Nijar.
Sanarwar ta kara da cewa kawo yanzu an kama wadanan mutane da wadanda suka hada kai da su kuma tuni aka sanar da alkali mai shigar da kara wanda a take ya kaddamar da bincike.
An wayi garin ranar Alhamis 19 ga watan Oktoba cikin yanayin rudani sakamakon rashin sanin takamaimen abin da ya faru bayan da dogarawan fadar Shugaban kasar Nijar suka kai samame a unguwar Tchangarey da ke kwaryar birnin Yamai da sanyin safiya inda aka yi ta harbe-harben bindigogi kafin daga bisani wasu rahotanni suka danganta lamarin da wani abin da ya wakana a fadar shugaban kasa.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna