Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bankado Sabbin Bayanai Kan Zargin Bazoum Da Yunkurin Tserewa


Hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum
Hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum

Hukumomin shari’ar jamhuriyar Nijar sun sanar cewa binciken da suka gudanar ya bada damar gano wasu karin bayanan  da ke gaskanta zargin yunkurin tserewar shugaba Mohamed Bazoum da iyalinsa. Sun ce sun kama kudade da dama da wasu tarin kayayaki a fadar ta hambararren shugaban.

Da yake bayani a gidan talabijin din RTN mallakar gwamnatin Nijar alkali mai shigar da kara a kotun daukaka kara ta birnin Yamai Salissou Chaibou, ya ayyana cewa bayanan da suka tattara sun gano cewa an dauki hotunan barikin dogarawan fadar shugaban kasa da suke zargin hambararren shugaban kasar ya tura wa Faransawa. Sannan ya ce sun bankado tsarin da aka kitsa a kokarin tantance filin da jiragen sama masu saukar ungulu zasu sauka su dauki shugaban da iyalinsa domin kaisu birnin Kebbi.

Mai shari’a Salissou Chaibou ya kara da cewa binciken kayayyakin da aka kama a hannun masu yunkurin tserewar da wanda aka gudanar a fadar shugaba Bazoum sun bada damar kama makudan kudade da kadarori masu daraja, da suka hada da million 86,250.000 na CFA, dalar Amurka 17,017, Euro 3,835 da pam 5 na Engila, CD 16 na Ghana, zinare gram 2,800, azurfa gram 333, komfitoci 3, na’urar daukar hoto 1, wayoyin hannu 13, layukan waya masu yawa, da takardun filaye kimanin 25, da dai wasu wayoyi sama da 10 da aka lalata, da bindiga samfarin Bereta da sauran kayayaki.

Sannan an kama kudade million 68 na CFA da kudaden kasashen waje a hannun wasu dogarawan fadar shugaban kasa da ake zargi da hannu a yunkurin tserewarsa.

Wani na hannun daman hambararren shugaban kasar Sahanine Mahamadou, da ke maida martani akan wadanan zarge zarge, na kallon abin a matsayin yunkurin shafa kashin kaji.

To amma a ra’ayin shugaban kungiyar GRAZ Gayya Salissou Amadou, na ganin bai kamata a yi gaggawar yanke hukunci kan bayanan na hukumomi ba.

A ranar 20 ga watan Oktoban da ya gabata ne majalissar sojoji ta CNSP ta bada sanarwar dakile yunkurin tserewar shugaba Mohamed Bazoum da iyalinsa, da jami’an tsaronsa 2, har ma da masu dafa masa abinci su 2, lamarin da ya haifar da babbar muhawara a tsakanin ‘yan kasa.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG