Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ci Karfin Ayyukan Kwashe Sojojin Faransa Daga Nijar


France Mali
France Mali

Rundunar mayakan Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa an fara cin karfin ayyukan kwashe dakarun Faransa daga kasar ta Nijar.

Wannan ya biyo bayan wata 1 bayan kaddamar da ayyukan ficewarsu kamar yadda hukumomin mulkin sojan CNSP suka nuna bukata bayan da suka yanke shawarar tsinke huldar ayyukan tsaro da kasar Faransa a washegarin kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum.

A sanarwar da rundunar mayakan Nijar ta saba fitarwa a kowane mako 2 dangane da ayyukan baraden kasar a fagen. Daga nan aka bayyana halin da ake ciki game da ayyukan kwashe sojojin Faransa daga kasar, kawo yanzu dakaru 909 daga cikin 1500 din da Faransar ta girke a Nijar suka fice daga wannan kasa hade da dimbin kayan yakin walau ta jirgin sama ko ta hanyar kasa a tsawon makwanni 4 da aka yi ana gudanar da wannan aiki da sojojin juyin mulkin Nijar suka kira yunkurin kwatar wa kasa cikakken ‘yancin kai.

Samun irin wadanan nasarori cikin kankanen lokaci wani abin alfahari ne ga al’ummar Nijar a gwagwarmayar ganin sojojin Faransa sun fice daga kasar inji Habila Rabiou, daya daga cikin jagorin matasan da suka yi tsayin daka a fafutikar cimma wannan manufa.
Tuni dai aka kammala kwashe dukkan askarawan Faransar da ke da sansani a garuruwan Ouallam da Tabaibare na jihar Tilabery iyaka da kasar Mali inji hukumomin tsaro. Abinda ke nufin a halin yanzu hankali ya karkata wajen sansanin sojan sama da ke birnin Yamai wato Escadrille.

Akwai alamar yiyuwar komai zai kammala kafin shudewar wa’adin da ke cika a ranar 31 ga watan disamban 2023.
A washegarin juyin mulkin 26 ga watan Yuli ne Majalisar Sojojin CNSP ta tsinke huldar ayyukan tsaro da Faransa saboda haka ta bukaci ta kwashe Sojojinta 1500 da ta girke a Nijar a shekarar 2015 bayan da kungiyoyin ta’addancin Mali suka fadada ayyukansu zuwa makwafciyar kasa.
Faransa da ke ikirarin zuwa yankin Sahel don murkushe matsalolin tsaro ta fuskanci suka daga al’umomin Mali da Burkina Faso da Nijer saboda zarginta da hada baki da ‘yan ta’adda zargin da hukumominta suka sha musantawa.
Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG