Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Gangamin Nuna Bukatar A Hukunta Mukarraban Hambararriyar Gwamnatin Nijar


Zanga-zanga a Nijar
Zanga-zanga a Nijar

Kungiyoyin farar hula sun yi gangami ranar Lahadi a birnin Yamai da nufin nuna bukatar mahukunta su kadammar da farautar mukarraban gwamnatin PNDS Tarayya, cikinsu har da shugaba Issouhou Mahamadou da suke zargi da handamar dukiyar kasa, sai dai magoya bayan tsohon shugaban sun yi watsi da batun.

Gwamman mazauna birnin Yamai ne suka yi jerin gwano daga dandalin Place de la Concertation dab da majalisar dokokin Nijar zuwa harabar kotun Tribunal da ke mahadar hanya wato Rond Point Justice a birnin Yamai, inda suka gudanar da gangami. Suna masu Shewa da kiraye kirayen nuna bukatar ganin hukumomin mulkin sojan kasar sun fara hukunta mutanen da su ke yi wa kallon mahandama daga cikin kusoshin hambararriyar gwamnati.

Zanga-zanga a Nijar
Zanga-zanga a Nijar

Gamatche Mahamadou, shi ne jagoran kungiyoyin da suka yi kiran a fito. Ya ce duk wata barnar kudi da almundahana da aka yi a Nijar, tsohon shugaba Issouhou Mahamadou na da hannu kuma ya kamata a kama shi a kuma hukanta shi.

To sai dai mukarraban tsohon shugaban kasar na ganin tuni masu zanga zangar suka sami amsa daga al’ummar Yamai, bisa la’akari da yadda suka yi buris da gayyatar zuwa gangami, inji wani tsohon dan majalisar dokokin kasa Abdoul Moumouni Ghousmane, wanda ke daukar zargin kungiyoyin a matsayin mara tushe.

Zanga-zanga a Nijar
Zanga-zanga a Nijar

Ganin yadda ba su sami amsa ba daga hukumomi masu fafutikar sun lashi takobin ci gaba da fitowa kan titi har sai hakarsu ta cimma ruwa.

A wani labarin da ke da alaka da sabon babin siyasar da aka shiga a Nijar, shugaban jam’iyyar PNPD kuma dan takara a zaben shugaban kasa na 2020 Intinicar Alhassan, ya shiga yajin dauke numfashi ranar Lahdi 5 ga watan Nuwamba, sannan a dayan gefen ya yi kiran jama’a su shiga kade kade ta hanyar amfani da kwanoni da cokali da nufin tayar da kwaramniyar nuna bukatar a sallami hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum, domin a cewarsa yin hakan wani mataki ne na kare dimokradiyya, yayin da a ranar Litinin ake sa ran kotun ECOWAS da ke Abuja za ta fara sauraron bahasi daga bangarorin da ke takun saka bayan juyin mulkin 26 ga watan Yuli.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG