Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIJAR: Ana Takun Saka Tsakanin Gwamnatin Jiha Da 'Yan Fafatika


Sojojin Juyin Mulkin Nijar
Sojojin Juyin Mulkin Nijar

Wadansu kungiyoyin fararen hula masu goyon bayan sojojin CNSP a Jamhuriyar Nijar sun bayyana rashin jin dadinsu kan yadda suka ce gwamnan Yamai ya na masu katsalandan a harkokin cikin gida.

Kungiyoyin sun yi wannan zargin ne bayan da suka kaurace wa wani taron karkasa kudaden tallafin da ‘yan diaspora suka aike da zummar karfafa guiwar ‘yan gwagwarmayar tabbatar da sabuwar tafiyar da kasa ta sa gaba biyo bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.

Rashin gamsuwa da tsarin da aka yi amfani da shi wajen rarraba wasu kudade million 100 na cfa da ‘yan Nijer mazauna Togo suka turo gida a matsayin gudunmowa ga masu gwagwarmayar kare martabar kasa sanadiyar takun sakar da ke tsakanin hukumomin CNSP da kungiyoyi irinsu CEDEAO da EU da dai sauransu ya sa kawancen kungiyoyi na Front Patriotique pour la Souverainete FPS kauracewa zaman kasafta wadanan kudade kamar yadda wani jigonsu Bana Ibrahim ya bayyana a taron manema labaran da suka kira.

Masu goyon juyin mulkin Nijar (AP)
Masu goyon juyin mulkin Nijar (AP)

Wannan mataki bai yi wa mahukunta dadi ba inji kungiyoyin na FPS musamman gwamnan Yamai Janar Abdou Assoumane a bisa la’akari da wa wasu kalaman da ba suka ce ya furta.

To amma wani dan farar hular na daban Ibrahim Namewa na kungiyar RPDS da ke bayyana ra’ayinsa kan wannan dambrawa ya gargadi takwarorinsa ‘yan fafutika akan maganar kwatanta gaskiya.

Masu goyon bayan juyin mulkin Nijar
Masu goyon bayan juyin mulkin Nijar

A ranar 2 ga watan satumba 2023 ne, kungiyoyin fararen hula suka yi zaman dirshe a harabar sansanin sojan Faransa da nufin jaddada bukatar ficewar dakarun Faransar daga Nijer abin da ya sa ‘yan kasar mazauna kasashen waje suka yi ta aiko da gudunmowar kudade har ma da ta cimaka da suka hada da shinkafa, sai dai wasu daga cikin iriin wadanan kungiyoyi sun nuna damuwa kan yadda wasu takwarorinsu suka mayar da wannan fafutika tamkar wata hanyar samun kudaden shiga.

Saurari cikakken rahoton:

Ana Takun Saka Tsakanin Gwamnati da 'yan Fafatika.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG