A yayin da ake cika watanni uku da juyin mulkin da ya yi sanadin da kungiyar CEDEAO da UEMOA suka kakaba wa Jamhuriyar Nijar jerin takunkumi, gamayyar kungiyoyin goyon bayan sojojin CNSP ta kudiri aniyar maka wasu daga cikin shugabanin kasashen yammacin Afrika a kotun kula da ‘yancin dan adam da kare muradun al’umomin nahiyar Afrika.
Kungiyoyi za su dauki wannan mataki ne saboda shugabannin kasashen da hannu a wahalhalun da jama’ar ta Nijar ke fuskanta.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da Patrice Talon na Jamhuriyar Benin da wasu takwararorinsu na kasashen CEDEAO da ba a ambaci sunayensu ba ne gamayyar kungiyoyin Front Patriotique pour la Souveraite ke shirin shigar da kararsu a gaban kotun kare hakkin dan adam da na al’umomin Afrika cour Africaine des Droits de l’Homme et des Peuples.
Suna zarginsu da toye hakkin ‘yan Nijar ta hanyar jerin takunkumin da ECOWAS da UEMOA suka kakaba wa kasar bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin dimokradiya.
Tuni dai aka fara yunkurin tattara bayanan da za a gabatar wa kotun a matsayin hujojin da ke tabbatar da cewa matakan da CEDEAO da UEMOA suka daukan kan Nijar suna cutar da ‘yan kasar.
A 1998 ne aka kafa kotun Afrika mai kula da kare hakkin dan adam da na al’umomi mai ofishi a birnin Arusha na kasar Tanzania a karkashin inuwar kungiyar tarayyar Afrika da nufin karfafa matakan kare hakin dan adam. kasashe 34 ne suka yi rajista a matsayin mambobinta sai dai daga cikinsu 8 kacal ne suka yi amanna da hurumin kotun.
Najeriya da Benin na daga cikin kasashen da har yanzu ba su yi amanna da huruminta ba abin da ke nufin ba ta da karfin gurfanar da irin wadanan kasashe in ji masana sha’anin diflomasiya.
Saurari rahoto:
Dandalin Mu Tattauna