La’akari da halin kuncin da matakin na ECOWAS ya jefa jama’ar Nijer, har ma da na wasu kasashe mambobin kungiyar, ya sa wasu kungiyoyi shirya wannan zama don ankarar da shugabanni.
Dandazon mutane da suka hada da maza da mata da matasa har ma da daliban makarantun boko ne suka hallara a harabar reshen kungiyar kasashen Afrika ta Yamma wato CEDEAO a wannan Laraba 8 ga watan Nuwamba a bisa gayyatar wasu kungiyoyin fararen hula, suna masu furta kalamai irin na nuna fusata akan matakin da shugabannin yankin suka dauka a matasyin na ladabtar da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar a bisa la’akari da yadda abin ya shafi talakkawa wadanda a kulliyaumin rayuwarsu ke kara tsanani.
Rufe iyakokin Nijar da kasashen Najeriya da jamhuriyar Benin shi ne mataki mafi tasiri a jerin takunkumin na ECOWAS, harakokin kasuwanci da zirga zirga sun matukar fuskanci koma baya sabili kenan da al’umomin kasashen CEDEAO mazauna Nijar su ka shiga wannan tafiya ta neman shawo kan shugabanin yankin su kalli halin da ake ciki da idon rahama.
Wannan na wakana ne a wani lokacin da kotun CEDEAO ta ayyana ranar 21 ga watan nan na Nuwamba a matsayin ta zaman sauraren bangarori bayan da mahukutan Nijar suka shigar da karar kungiyar ECOWAS wace suke zargi da wuce gona da iri a takunkumin da ta kakaba wa kasar bayan kifar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum yayin da a daya bangare wasu rahotanni suka ayyana cewa ministan tsaron kasar Nijar, janar Salifou Mody, a yayin ziyara da ya kai kasar Togo a ranar Litinin din da ta gabata, ya sanar cewa hukumomin rikon kwarya sun bukaci shugaba Faure N’gnassimbe ya shiga gaba domin duba hanyoyin sulhunta kace nacen da ke tsakanin CEDEAO da Nijar.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna