Mutane kimanin 35 ne shugaban majalissar CNSP Janar Abdourahamane Tchiani ya nada a matsayin mambobin hukumar COLDEFF mai alhakin yaki da cin hanci da farautar mahandama dukiyar kasa.
Wadannan mutane sun hada da hafsoshin sha’anin tsaro 10, da farar hula 25, ciki har da lauyoyi, da alkalai, da masana harkar tattalin arziki, da kuma wasu 'yan fafutika na kungiyoyi masu zaman kansu.
Wannan wani matakin share fage ne a yunkurin da hukumomin mulkin sojan suka sa gaba domin soma binciken almundahanar da ake zargin an tafka a zamanin gwamnatocin da suka gabata. A ra’ayin wani dan siyasa, Alhaji Assoumana Mahamadou, daga yanzu kallo ya koma sama.
Shugaban kungiyoyin farar hula na Reseau Esperance Bachar Mahaman, wanda ya bayyana gamsuwa da kwarewar da dama daga cikin jami’an hukumar ta COLDEFF, na da shakku kan cancantar wasunsu domin yaki da cin hanci babbar magana ce da ke bukatar sanin makamar aiki inji shi.
Samun nasarori a ayyukan wannan hukuma abu ne da ya danganta da wasu muhimman matakai da ya kamata a dauka tun yanzu.
A nan gaba ne mambobin hukumar ta COLDEFF za su yi rantsuwar kama aiki, koda yake kawo yanzu ba a tsayar da rana ba a hukunce.
Yaki da cin hanci a Nijar wani abu ne da a baya ya zame wa gwamnatoci karfen kafa sakamakon yadda jam’iyyun siyasa ke fakewa da kawance don kare mukarrabansu daga dukkan wani yunkurin mashara’anta, a saboda haka ‘yan kasa ke fatan ganin a irin wannan lokaci na gwamnatin rikon kwarya mahukunta za su kwatanta yi wa tufka hanci.
Saurari rahoton cikin sauti:
Dandalin Mu Tattauna