Bazoum Mohamed yace sakamakon zaben ‘yan majalisar dokoki ya yi nuni da cewa jam’iyar PNDS da kawayenta na da rinjaye a sabuwar majalisar dokoki domin muna da kujeru 129 daga cikin kujerun wakilci 166
Jam’iyyun da suka zo na uku da hudu a zagayen farko na babban zaben shugaban kasa a jamhuriyar Nijar, sun bada sanarwar hada kai tare da mara wa dan takarar jam’iyyar PNDS mai mulki baya.
Hukumar yaki da cin hanci a jamhuriyar a Nijer ta bada sanarwar kwato wasu makudan kudaden haraji da suka makkkale a hannun wasu kamfanoni da masana’antun da ake zargi da turjewa ma’aikatar harajin kasar.
Shuwagabanin Hukumar zaben jamhuriyar Nijer sun gana da jakadun kasashen waje da wakilan kugiyoyin kasa da kasa a yau da hantsi domin tantauna hanyoyin da za a tunkari zagaye na 2 na zaben shugaban kasar da za a gudanar ranar 21 ga watan fabrerun dake tafe.
Kungiyoyin rajin kare dimokradiya sun kaddamar da ayyukan fadakar da jama’a tare da tunatar da masu hannu akan sha’anin gudanar da zabe
A Jamhuriyar Nijar kotun tsarin mulkin kasar ta tabbatar da dan takarar PNDS Tarayya Bazoum Mohamed da Mahamane Ousmane na RDR Canji a matsayin wadanda za su fafata a zagaye na biyu na zaben ranar 21 ga watan Fabrairu.
Kotun tsarin mulkin jamhuriyar Nijer ta bayyana sakamakon dindindin na zaben shugaban kasa da ya gudana a ranar 27 ga watan Disamba da ya gabata, sai dai kotun ta ce daga cikin ‘yan takara 30 da suka fafata a zagayen na farko ba wanda ya sami sama da kashi 50 daga cikin 100 na kuri’u.
A Jamhuriyar Nijer an bude bikin kaddamar da wata cibiyar kasuwancin albasa a birnin Yamai da nufin karfafa hanyoyin baiwa manoman albasa da masu kasuwancinta damar cin moriyar wannan sana’a.
Jami’an tsaron Jamhuriyar Nijar sun bankado wata kasuwar fataucin makamai ta bayan fage a jihar Tahoua da ke Arewacin kasar lamarin da ya ba da damar kama wasu tarin bindigogi da harsashai.
Jami’an tsaro a jamhuriyar Nijer sun kama wani direban motar daukar marasa lafiya dauke da lodin tabar wiwi yayin da ya ke kan hanyar komawa birnin Tahoua bayan da ya ajiye wani mara lafiya a asibitin birnin Yamai.
Wasu ‘yan takara 10 daga cikin wadanda suka fafata a zagayen farko na zaben shugaban kasa da ya gudana a ranar 27 ga watan Disamban shekarar 2020 sun fara tattaunawa da ‘yan takarar da zasu kara a zabe zagaye na biyu ranar 21 ga watan Fabarairu da ke tafe.
A karon farko bayan shafe shekaru, jam’iyyun adawa a Jamhuriyar Nijer sun aika da wakilansu zuwa hukumar zaben kasar yayin da aka tunkari zaben shugaban kasa a zagaye na biyu.
Jam'iyyun adawa na kalubalantar zaben shugaban kasar jamhuriyar Nijar zagaye na farko.
A jamhuriyar Nijar, yayin da ake tunkarar zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 21 ga watan Fabrerun wannan shekarar ta 2021, jam’iyyun kawancen da suka mara wa dan takarar PNDS Bazoum Mohamed sun kara jaddada matsayinsu don ganin dan takarar ya lashe zaben.
Alkaluman hukumar CENI na nunin za a fafata a zagaye na 2 a ranar 21 ga watan Fabreru a tsakanin dan takarar PNDS Tarayya Bazoum Mohamed da Mahaman Ousaman na jam’iyyar RDR ta ‘yan hamayya.
Hukumar zabe a jamhuriyar Nijer ta bayyana cewa, akwai yiyuwar a cikin daren yau alhamis ta kammala tantance alkaluman karshe da suka rage daga cikin wadanda ake jiran shigowarsu daga gundumomi 266 na kasar.
Hukumomin kiwon lafiya a jamhuriyar Nijer na ci gaba da kara jan hankulan al’umar kasar game da batun mutunta ka’idodin da aka shimfida da nufin dakile anobar covid 19, bayan la’akari da yadda yawan wadanda suka harbu da kwayar cutar ke karuwa a kulli-yaumin.
An bayyana zaben shugaban kasar da aka gudanar a Jamhuriyar Nijar a matsayin abin koyi.
A yayin da ya rage ‘yan sa’oi kadan a gudanar da zagayen farko na zaben shugaban kasar Nijer hade da na ‘yan majalisar dokoki, kungiyoyi masu zaman kansu na ci gaba da kara jan hankulan jama’a don ganin komai ya gudana cikin kwanciyar hankali.
Domin Kari