Jam’iyyun adawa a Jamhuriyar Nijar, sun bukaci a soke sakamakon zaben yankunan da suke zargin an yi satar zabe, a yayin zagayen farko na zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki da aka gudanar a ranar 27 ga watan Disambar 2020.
Suna masu cewa akwai bukatar girke sojoji a runfunan zabe, a yayin gudanar da zabe zagaye na 2 da za a yi a ranar 21 ga watan Fabrairu, don kaucewa faruwar matsalolin da aka ci karo da su a baya.
Zauren Palais du 29 Juillet kenan a yammacin jiya Litinin inda jam’iyun kawancen hamayya na CAP 2021 suka gudanar da gangami da nufin bayyana matsayinsu a hukumance game da sakamakon wucin gadi, na zagaye na farko na zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki.
A wata sanarwar da suka fitar, gamayyar jam’iyyu sun yi watsi da sakamakon yankunan da suka ce an tafka magudi, wadanda suka hada da wasu da’irorin jihar Tahoua da Arewacin jihohin Maradi Zinder da Diffa. Maman Sani Adamou shine kakakinsu.
Jam’iyun kawancen CAP 2021 sun bukaci a sake shirya zabe a wuraren da aka yi fama da irin wadanan matsaloli zaben da ya gabata, duk kuwa da cewa har yanzu kotun tsarin mulkin kasa ba ta bayyana matsayinta ba a game da sakamakon wucin gadin, da hukumar CENI ta fitar a ranar Asabar 2 ga watan Janairu.
A cewarsu girke sojoji a runfunan zabe ita ce hanya mafi a’ala wajen kaucewa faruwar abubuwan da suka wakana a zagayen farko.
A game da zagaye na 2 na zaben da za a gudanar a ranar 21 ga watan Fabrairu, jam’iyun hamayya sun jaddada goyon baya ga dan takararsu tsohon shugaban kasa Mahaman Ousman, na jam’iyar RDR canji, wanda tun a zagayen farko ya sami goyon baya daga jam’iyar Moden Lumana ta Hama Amadou, da UDR Tabbas ta Amadou Boubacar Cisse.
Sai dai a ta su sanarwar da suka fitar a makon jiya, jam’iyyun kawancen goyon bayan dan takarar jam’iya mai mulki Bazoum Mohamed, sun ce suna da kwarin gwiwar lashe zagayen na 2 domin dora shi akan karagar mulki.
Don karin bayani ga rahoton a cikin sauti.