Wannan sana'a ta sa Nijir din ta yi fice a kasashen waje saboda ingancin albasar da ake nomawa a karkarar Galmi dake jihar Tahoua.
Noman albasa na kan gaba a sahun ayyuka da sana’oin da suka fi samar da kudaden shiga a kasar Nijar amma lura da yadda abubuwan ke gudana cikin wani yanayi irin na karazube ya sa shugabannin manoma da masu kasuwancin albasa kafa cibiyoyin kasuwancin albasa a wasu mahimman wurare cikinsu har da birnin Yamai.
Wannan na matsayin wani matakin share fage a yunkurin soma sarrafa albasa zuwa wasu nau’o’in cimaka na daban.
Ta wani bangaren cibiyoyin kasuwancin albasa wani tsari ne da ke hangen takaita ko kuma kawo karshen asarar da manoman albasa da masu kasuwancinta ke tafkawa saboda yadda a can baya harakokin ke gudana a gargajiyance inji Alhaji Abdulkader Issaka shugaban cibiyar kasuwancin albasa ta birnin yamai.
Shugaban kungiyar manoman albasa daga tarayyar Najeriya da ya jagoranci wata tawagar manoman albasa a taron kaddamar da wannan cibiya yace sun zo da wasu mahimman shawarwari.
Ga Souley Moumouni Barma da karin bayani: