Wadannan ‘yan takara da tuni su ka kafa kungiyar kawance mai suna Alliance des Candidats pour le Changement ko ACC a takaice, sun ce za su saurari bahasi daga kowanne daga cikin ‘yan takarar da zasu kara a zaben ranar 21 ga watan Fabarairu, wato Mahaman Ousman na jam’iyyar adawa ta RDR Canji da Bazoum Mohamed na PNDS Tarayya mai mulki domin tantance manufofin kowanne daga cikinsu kafin su yanke shawara game da wanda zasu ba kuri’unsu.
Kakakin kungiyar kawancen Abdourahamane Oumarou ne ya bayyana hakan a yayin wata ganawa da tawagar kungiyar da dan takara Mahaman Ousman, inda ya ce tun lokacin da su ka kulla wannan kawance sun saurari kowa.
Ya kuma ce za su saurari dukkan 'yan takarar kuma za su ji abinda za su yi wa kasa, bayan haka za su duba su gani wanene daga cikinsu zai yi abinda 'yan kasar ke so.
Mahaman Ousman ya yaba da wannan yunkuri wanda a cewarsa alama ce ta fahimtar tsarin tafiyar siyasa.
A nan gaba kawancen ‘yan takarar na ACC ke shirin ganawa da dan takara Bazoum Mohamed domin jin manufofin siyasar da ya sa gaba kafin daga bisani su sanar da jama’a sunan wanda suka ga ya fi dacewa a zaba a ranar 21 ga watan Fabarairun 2021 a tsakanin dan takarar PNDS Tarayya mai mulki da dan takarar RDR Canji ta ‘yan hamayya.
Saurari cikkaken rahaton cikin sauti: