Jami’yar Moden Lumana ta jagoran ‘yan hamayya Hama Amadou a Jamhuriyar Nijer ta umurci magoya bayanta su kadawa tsohon shugaban kasa Mahaman Ousman kuri’a a zagayen farko na zaben shugaban kasar na ranar Lahadin dake tafe abin da ke zama tamkar wani matakin kara jan damara a wannan fafatawa.
Yayin da ya rage mako a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki a Nijer, kungiyoyin fararen hula na ci gaba da jan hankulan ‘yan kasar game da muhimmancin zabe nagari.
Kungiyar nakasassu a Jamhuriyar Nijar ta gudanar da taron addu'o'i don neman zaman Lafiya yayin zaben da za a yi na shugaban kasa da na 'yan majalisa.
Ofishin jakadancin Amurka a Jamhuriyar Nijar ya bayyana gamsuwa da yanayin da aka gudanar da zaben kananan hukumomi na ranar 13 ga watan Disamba a fadin kasar ta Nijar
Yayin zagayowar ranar da kasar Nijer da ta Faransa su ka yi asarar wasu sojojinsu, kungiyoyin fafatuka sun sake zaburar da batun shari'ar zargin cin kudin tsaro, wadda su ke zargin ana neman a shiriritar da ita.
A yayin da yakin neman zabe ke kara kankama a jamhuriyar Nijar gamayyar kungiyoyin fararen hula ta COCEN da hadin gwiwar kungiyar Tarayyar Turai sun shirya wani taron horo domin karawa jami’an fafutika dabarun saka ido akan sha’anin zabe ta yadda zasu tantance zahirin yanayin zaben da za a yi.
Kwamitin dattawan Nijer ya yi kira ga dukkan bangarorin da ke da hannu a sha’anin tsara zabe su dauki matakan da za su bada damar gudanar da komai cikin haske da adalci ba tare da nuna wa kowane dan kasa wariya ba.
Kwararru da masharhanta sun ce taron zai taimaka wajen karfafa zaman lafiyar al'uma da kuma inganta dangantaka tsakanin jami'an tsaro da matasa.
Shugabannin hukumar zabe sun gana da wakilan jam’iyun siyasa a Jamhuriyar Nijer domin sanar da su halin da ake ciki game da tsare-tsaren zaben kananan hukumomi na ranar 13 ga watan Disamba mai zuwa.
Kungiyar ‘yan jarida a Nijer ta koka a game da yadda anobar COVID-19 ta raba wasu ma’aikatan kafafen yada labarai masu zaman kansu da aiki sanadiyyar karancin kudaden shiga.
A jamhuriyar Nijer majalisar ministocin harkokin wajen kasashen Musulmi mambobin kungiyar OIC ta kammala zamanta karo na 47 a yammacin ranar Asabar 28 ga watan Nuwamba bayan shafe kwanaki 2 ta na tattaunawa a game da halin da ake ciki a wadanan kasashe.
A Jamhuriyar Nijar an yi jana’izar tsohon shugaban kasa Tandja Mamadou a fadar shugaban kasa inda daruruwan mutane suka hallara.
Daukacin Janhuriyar Nijar, kama daga mahukunta da magabata zuwa talakawan kasar da ma na kasashen ketare, na cigaba da alhinin rasuwar tsohon Shugaban Janhuriyar Nijar, Tandja Mamadou.
Majalisar Dinkin Duniya ta shirya wani taron hadin gwiwa da kungiyoyin kasa da kasa a Jamhuriyyar Nijar da suka hada da kunigiyoyin EU, ECOWAS da CENSAD da nufin jan hankulan bangarorin siyasar kasar kan batun zaman lafiya game da tsare tsaren zabukan watan Disamba mai zuwa.
Yayin da kasuwar mai ke cigaba da fuskantar kalubale a duniya, kasashen Afurka masu arzikin man fetur sun shiga wani babban taro a Janhuriyar Nijar na duba hanyoyin kare darajar albarkatun mansu.
A jamhuriyar Nijer ‘yan kasar na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu bayan da a karshen makon jiya kotun tsarin mulkin kasar ta bayyana sunayen mutanen da suka cancanci shiga zaben shugaban kasa na ranar 27 ga watan Disamba.
Hukumomin kiwon lafiya a jamhuriyar Nijer sun bayyana shirin kara tsaurara matakan dakile annobar COVID-19 bayan da aka gano wasu mutane da dama da suka harbu da kwayar cutar a makon jiya, saboda haka aka gargadi jama’a a kan maganar mutunta ka’idodin kare kai daga wannan anoba.
A Jamhuriyyar Nijer kotun tsarin mulkin kasar ta bayyana sunayen mutanen da suka cancanci shiga zaben shugaban kasa na ranar 27 ga watan Disamba da ke tafe bayan gudanar da aikin tantancewa amma kuma ta yi watsi da wasu daga cikin 'yan takarar.
Wasu magoya bayan jam’iyyun adawa a Jamhuriyar Nijar sun shigar da kara a kotun Diffa da nufin kalubalantar dan takarar jam’iyyar PNDS Tarayya Bazoum Mohamed.
A Jamhuriyar Nijar wata sabuwar mahawara ta barke a game da makomar takarar jagoran ‘yan adawar kasar Hama Amadou.
Domin Kari