Karon farko kenan da shugabanin hukumar zabe ke irin wannan ganawa da jakadun kasashen waje da wakilan kungiyoyin kasa da kasa tun bayan gudanar da zaben kananan hukumomi da na ‘yan majalisar dokoki hade da na shugaban kasa na watan disamban da ya gabata.
Bangarorin sun fara wannan zama da bitar babban zaben na Nijer kafin su tantauna akan tsare tsaren zagaye na 2 na zaben shugaban kasa na ranar 21 ga watan fabreru.
A cikin hirar shi da Muryar Amurka, mataimakin shugaban hukumar zabe Dr Aladoua Amada ya bayyana cewa, makasuddin taron shine don a bayana nasara da aka samu da kuma kurakuren da aka samu don a gyara.
Jakadun kasashen da wakilan kungiyoyin kasa da kasar da suka halarci wannan taro sun jaddada aniyar ci gaba da dafawa jamhuriyar Nijer don ganin an gudanar da zaben mai zuwa cikin kyaukyawan yanayi.
nijar-ana-wayar-da-kan-jama-a-kan-zagaye-na-biyu-na-zabe
a-karon-farko-jam-iyyun-adawa-a-nijar-sun-aika-da-wakilansu-hukumar-zabe
jam-iyyun-adawa-na-kalubalantar-zaben-shugaban-kasar-nijar
Saurari cikakken rahoton Souley Mummuni Barma cikin sauti sauti: