Jam;'iyyun sun aika wakilansu hukumar zaben kasar ne, a wani abin da suka kira yunkurin toshe hanyoyin magudin zabe.
Kusan shekara sama da uku jam'iyyun suka kwashe suna kauracewa ayyukan hukumar, saboda a cewar su haramtacciya ce.
Tun a washe garin zagayen farko na zaben shugaban kasa da ya gudana a ranar 27 ga watan Disamba na 2020, jam’iyun kawancen hamayya na CAP 20 21 suka kudiri aniyar aika wakilansu hukumar zaben kasar, bayan da suka gano cewa rashin aika mutanen da za su wakilcesu akan kuri’u da aka kada ya taimakawa jam’iyar PNDS mai mulki wajen murda sakamakon zaben a cewar jam’iyar.
Ita day PNDS ta musanta aikata ba daidai ba a zaben da ya gudana tana mai cewa zafin kaye ne ya sa 'yan adawa suke wadannan kalamai.
Hakan ya sa suka gaggauta tura wakilansu, wadanda shugaban Nijer ya sanya wa hannu akan takardar tabbatar da wakilicinsu a hukumar ta CENI, kamar yadda kakakin kwamitin yakin zaben ‘yan adawa Bana Ibrahim ya bayyana.
Jam’iyar PNDS Tarayya ta yi na’am da wannan mataki da take kallo a matsayin wani ci gaba a kokarin hada kan bangarorin siyasar kasar, bayan shafe shekaru a kalla 3 ana kace-nace a game da hallacin hukumar CENI inji wani mai magana da yawun jam’iya mai mulki Adamou Manzo.
Su ma ‘yan rajin kare dimokradiya sun yaba da wannan yunkuri na ‘yan adawa. Jami’i a kungiyar OPEL mai aikin sa ido a sha’anin zabe, Salissou Amadou ya ce, samin wakilcin bangarori a hukumar zabe hanya ce da za ta kawar da dukkanin wani shakku.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma: