Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Yiwu A Fitar Da Sakamakon Zaben Nijar Jumma'ar Nan


 Hukumar Zaben Nijar
Hukumar Zaben Nijar

Hukumar zabe a jamhuriyar Nijer ta bayyana cewa, akwai yiyuwar a cikin daren yau alhamis ta kammala tantance alkaluman karshe da suka rage daga cikin wadanda ake jiran shigowarsu daga gundumomi 266 na kasar.

Mataimakin shugaban hukumar Dr Aladoua Amada ne ya bayyana haka a hirarshi da Muryar Amurka.

Wannan na nuni da cewa, akwai yiyuwar fitar da kammalalen sakamakon zaben da aka gudanar ranar lahadi 27 ga watan Disamba a gobe juma’a 1 ga watan janerun 2021.

hukumar-ceni-na-ci-gaba-da-tattara-sakamakon-zaben-nijar

an-gudanar-da-zabe-mai-inganci-a-jamhuriyar-nijar---cen-sad

yadda-shugaba-issoufou-bazoum-ousmane-suka-kada-kuri-unsu

Maitaimakin shugaban hukumar zaben ya bayyana cewa, i zuwa lokacin yin wannan hirar sun kallama tattara sakamakon zaben gudumoni 151, watau ke nan cikin gundumomi 266 sauran 105, kuma sauran wadannan da suka rage duka sun riga sun shiga hannun hukumar zabe, abinda ake jira kafin wallafa sakamakon shi ne a tantance shi kafin sanar da shi a kafofin sadarwa da suka hada da radiyo da talabijin na kasa.

Hukumar Zaben Nijar
Hukumar Zaben Nijar

Mataimakin shugaban hukumar Dr Aladoua Amada ya ce, bisa ga dokar kasa, bisa kudurin doka na 156, hukumar zabe tana da kwana biyar ta wallafa sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa, ta sanar da al'umma sakamakon zaben, ta wallafa shi kuma ta mika sakamakon zaben ga kotun koli mai kula da harkokin zabe.

Ya kuma kyautata zaton cewa, za a fitar da wannan samakon zaben domin 'yan kasa a duk inda suke da kuma duniya su sani.

Masu Aikin Sa Ido a Zaben Nijar Daga Kasashen Afirka.
Masu Aikin Sa Ido a Zaben Nijar Daga Kasashen Afirka.

Mataimakin shugaban hukumar zaben ya musanta cewa sun sami tsaiko a gudanar da aikin. Bisa ga cewarshi, suna fitar da samakon zaben ne bisa ga lokacin da suka same shi.

Saurari cikakkar hirar Mataimakin shugaban hukumar Dr Aladoua Amada da wakilin Sashen Hausa Souley Mummuni Barma.

Ya Yiwu A Fitar Da Sakamakon Zaben Nijar Jumma'ar Nan:3:30"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG