Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Nijer Sun Nisanta Kansu Daga Matakin Hana Man Fetur Shiga Mali Da Tankiyar Diflomasiyar Kasashen 2


Shugaban Kasar Nijer Bazoum Mohamed
Shugaban Kasar Nijer Bazoum Mohamed

Hukumomin jamhuriyar Nijer sun yi karin haske dangane da matakin dakatar da shigar da man fetur zuwa kasar Mali.

Wannan na zuwa ne biyo bayan yadda wasu 'yan Nijar su ka fara alakanta al'amarin da tankiyar diflomasiyar da ta barke a tsakanin kasashen biyu sanadiyyar furicin da fira ministan rikon kwaryar Mali ya yi a jawabinsa na taron MDD da nufin tsangwamar shugaban kasa Mohamed Bazoum na Nijer.

A Wata takardar da ya aike wa jami’an wasu daga cikin tasoshin binciken jihar Tilabery a ranar 21 ga watan Satumban 2022 darektan hukumar shigi da ficin kaya ya umurce su da su hana motocin dakon mai dake fitowa daga Najeriya su ratsa Nijer zuwa kasar Mali don dakile hanyoyin fasa-kwabri. Har ila yau a wannan Takarda babban darektan ya kuma umurci jami’ai su bai wa motocin rundunar MDD dake aikin tsaro a Mali wato Minusma damar ketara kasar don shigar da mansu zuwa Mali

Wannan ya haifar da mahawara a kafafen sada zumunta. lamarin da ya sa ministan kudi Ahamed Djidoud yi wa manema labarai bayanin abinda ke faruwa.

Ya ce "tun a ranar 9 watan nan na Satumba ne na soke takardun izinin ketara Nijer da man fetur zuwa kasar Mali domin kamfanin dillancin mai na kasa wato Sonidep ya koka a game da yadda masu daukan man fetur daga Najeriya don kai shi Mali ke juye abin a gidajen man Nijer da nufin kewaye wa hanyoyin biyan haraji to amma an yi katari lokacin da muka dauki matakin dakatar da fitar da man akwai motoci da dama da ke kan hanyar zuwa Mali sabili kenan muka yanke shawarar basu dama su tsallaka har ma jami’anmu suka yi masu rakiya zuwa iyaka."

"Bayan haka na umurci babban darektan ma’aikatar shigi da ficin kaya wato Douanes ya sanar da ma’aikatansa cewa matakin dakatar da fitar da man dake fitowa daga Najeriya zuwa Mali zai soma aiki abinda ya sa ya fitar da takarda a ranar 21 ga watan Satumba wanda wasu ke son mayar da shi tamkar wani matakin maida martani ga ‘yan uwanmu na Mali, katari ne kawai aka yi abubuwan nan 2 suka faru kusa da kusa. Ya kamata mutane su daina wani cece kuce maras digi."

Kakakin gwamnatin Nijer Tidjani Abdoukadri a sanarwar da ya bayar yace wannan mataki na dakatar da fitar da man fetur zuwa Mali bai shafi man da Nijer ke tacewa a gida ba kuma har gobe man Nijer zai ci gaba da shiga kasar ta Mali.

Kungiyoyin kare hakkin jama’a sun yaba da matakin gwamnatin wanda ko baya ga maganar yaki da masu fasa kwabri abu ne da zai yi tasiri a yaki da kungiyoyin ta’addancin da suka addabin kasashen sahel. Shugaban kungiyar Voix des sans Voix na da irin wannan ra’ayi.

Jinkirin bada labari da kokarin boye abubwan dake faruwa da ma yadda wasu jami’an gwamnati ke yi wa sha’anin sadarwa rikon sakainar kashi wani abu ne da ke bai wa masu yada labaran karya damar cin karensu ba babbaka a kafafen sada zumunta a nan Nijer.

Ga rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

XS
SM
MD
LG