Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar, Bankin Duniya Sun Kaddamar Da Sabon Shirin Samar Da Wutar Lantarki


Injinan Kamfanin Sarrafa Wutar Lantarki
Injinan Kamfanin Sarrafa Wutar Lantarki

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta kaddamar da wani shirin hadin gwiwa da Bankin Duniya mai lakanin “Haske” da nufin samar da wutar lantarki da makamashi a daruruwan garuruwan kasar.

NIAMEY, NIGER - Wannan wani yunkuri ne na kara yawan mutanen da za su amfana da wutar lantarki a cewar hukumomi.

Kimanin dalar Amurka million 317, kwatankwacin miliyon 200,000 na CFA ne za a kashe domin samar da wutar lantarki a birane da karkara ta hanyar wannan aiki.

Shirin zai shafi makarantu, asibitoci da wasu ofisoshin hukuma a wani yunkuri na fadada yawan mutanen da ke samun wutar lantarki daga kashi 19 cikin 100 na jama’ar Nijar mai yawan mutane miliyan 22 zuwa kashi 40 cikin 100 kafin shekarar 2025, a yayin da shirin ke fatan fadada yawan masu samun wutar zuwa kashi 60 cikin 100 a shekarar 2030.

Ministan makamashin Nijar, Alhaji Ibrahim Yacouba, ya ce sun tsara gina wayar wuta kilo 270 a wuraren da suka dace ta kamfanin Nigelec da ke samar da lantarki a birane, sannan a garuruwan da kamfanin Nigelec bai kai lantarki za a kai musu lantarki na musamman.

A dayan bangaren shirin zai maida hankali wajen kafa matsakaitan tashoshin samar da wutar lantarki da hasken rana a kauyuka kimanin 500 da birane 79, wadanda za a mayar da al’amuransu a hannun ‘yan kasuwa inji wakilin bankin duniya a Nijer Han Fraeters.

Fraeters ya ce wannan shiri na Haske mataki ne da ke hangen kare muhalli kuma dama ce ta kawo karshen bambancin da ake fuskanta a tsakanin maza da mata wajen samun damar cin moriyar wutar lantarki, har ma a wajen tafiyar da harkokin makamashi.

Ya kara da cewa wannan shiri zai bada muhimmanci wajen kara yawan matan da za su yi shugabanci a fannin makamashi musamman a kamfanin wutar lantarkin Nigelec, sannan shirin Haske zai bada damar kirkiro da hanyoyin ci gaban al’umma a fannoni da dama.

Mutane million 2 da rabi ne ake hasashen bai wa damar soma samun wutar lantarki a tsawon shekaru 5 na wannan shiri na Haske, wanda kashi 50 daga cikin 100 na kudaden da za a kashe wajen gudanar da shi ke matsayin tallafi, yayin da dayan kashi 50 din ke zaman rance da gwamnatin Nijer za ta biya a shekarun da ke tafe.

Saurari rahoton Souley Mumuni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG