Shugabannin sun bayyana haka ne a karshen wani taro da suka gabatar, inda suka shawarci hukumomin kolin kasar Nijer akan bukatar horar da matasan jihar ta Maradi akan dubarun tsaro ta yadda zasu bada gudunmuwa kwatankwacin yadda aka yi a wasu jihohin da aka yi fama da matsalolin tsaro.
Ganin yadda matsalolin tsaro ke kara ta’azzara a wasu gundumomin jihar Maradi yau shekaru kusan 4 ya sa shugabanin kungiyar Mafaliya Hadin Kai da na wasu takwarorinta masu fafutikar samar da ci gaban al’umma suka kira taro a birnin Yamai fadar gwamnatin Nijer don nazarin hanyoyin da za a bullowa wannan al’amari da ya jefa al’umma cikin halin zaman dar-dar a wannan yanki mai makwfataka da jihohin arewa maso yammacin Najeriya wato Katsina da Zamfara.
A hirar shi da Muryar Amurka, kakakin kungiyar Mafaliya Alhaji Daouda Tankama yace sun fitar da sanarwar ne ganin yadda a kullum ake jin labarin sace mutane ana kashewa da kuma dauke masu dukiyoyi.
Shigar da mazaunan yankin da ke dandana kudar wannan aika aika ta ‘yan bindiga wani mataki ne da shugabanin kungiyoyin da ke gaban wannan tafiya ke ganin zai taimaka a samo bakin zare saboda haka suka gargadi gwamnatin Nijer ta shigar da matasan jihar Maradi a yakin da ta kaddamar da ‘yan ta’adda.
A nasa bayanin, Dr Moussa Mahaman Maty shugaban kungiyar Muradi. yace ko a yanzu haka akwai matasa da ke taimakawa suna gadi da kibiya ko adda amma, yaki da 'yan fashi masu bindiga ya fi karfinsu.
Kungiyoyin sun kuma nuna bukatar amfani da hanyoyin ba sani ba sabo a ci gaba da neman mafitar tashin hankalin da jama’ar karkara suka tsinci kansu ciki sanadiyar lalacewar al’amuran tsaro.
Jihar Maradi na daga cikin yankunan da ke kan gaban mafi zaman lafiya da kwanciyar hankalin jama’a a Jamhuriyar Nijer har I zuwa shekarar 2019 lokacin da aka fara fuskantar aika aikar masu satar mutane don neman kudin fansa da barayin dabobi inda abin ya fara rikidewa zuwa kashe kashen fararen hula har ma da shugabanin al’umma.
Saurari rahoton a sauti: