Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Fafutika Sun Yi Gargadi Kan Bukatar Kafa Asusun Ajiyar Kason Kudaden Ma'adanai


Wasu masu hakar ma'adinai
Wasu masu hakar ma'adinai

A jamhuriyar Nijer kungiyoyin da ke bin diddigin sha’anin ma’adinai sun fara jan hankula a game da bukatar kafa asusun ajiyar wani kaso na kudaden shigar ma’adanai ta yadda watarana ‘ya'ya da jikoki za su mori wannan arziki a maimakon a bar su da irin illolin da ayyukan hakar ma’adanai ke haddasawa.

Masana sun tabbatar da cewa arzikin ma’adanai wani abu da ne da ko ba jima ko ba dade ka iya karewa daga karkashin kasar da ake hakarsa wanda kuma daga bisani a maimakon a ci gajiya sai dai neman hanyoyin mafitar matsalar gurbacewar muhalli da yanayin yankin da aka gudanar da wannan aiki.

La’akari da haka ne ya sa kundin tsarin mulkin Nijer ya tanadi dokar kafa asusun ajiyar wani kaso na kudaden shigar ma’adanai da zummar bai wa yara manyan gobe damar cin moriyar arzikin ma’adanai mafari kenan gamayyar kungiyoyin ROTAB ta fara tunatarwa akan wannan batu inji Mahamadou Tchiroma Aissami.

Asusun ajiyar kason kudaden ma’adanai wani abu ne da a wani zubin za a yi kwatantawa da wata inshorar cike gibi ko kuma na tunkarar wasu matsalolin bazata inji Saidou Ardji kwararre akan sha’anin ma’adanan karkashin kasa.

Matakin Karin kudin man diezel da hukumomin Nijer suka dauka a sanadiyyar mamayar Ukraine da Rasha ta yi da tsadar kayayyaki a kasuwanni ta dalilin wannan yaki abubuwa ne da ya kamata a dauki darasi daga faruwarsu.

A watan Maris din da ya gabata kamfanin Cominak na kasar Faransa ya bada sanarwar dakatar da ayyukan hakar uranium din da ya shafe shekaru sama da 40 ya na gudanarwa saboda dalilan da ake dangantawa da faduwar darajar uranium a kasuwannin duniya lamarin da ya jefa ma’aikata da mazaunan yankin cikin halin damuwa domin ba’idin matsalar tattalin arziki abin na shafar muhalli ayyukan noma da sha’anin kiwon lafiya sanadiyyar gurbacewar yanayi abin da ke kara fayyace mahimmancin kafa asusun ajiyar kason kudaden shigar ma’adanai.

Saurari rahoton Suleuman Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG