Matakin wanda ya biyo bayan wani binciken da aka gudanar a wasu makarantun horar da jami’an kiwon lafiya ya rutsa da wata makaranta daya a gundumar Gaya da makaranta daya dake gundumar Madaoua da wace ke gundumar Dogon Doutsi da wata 1 dake gundumar Ballayara da 1 a garin Dosso da daya a Yamai.
Dukansu masu zaman kansu wadanda aka gano su da rashin cike mahimman sharudan da suka zama wajibi kafin a bude irin wadanan makarantu.
Dr Iliassou Idi Mainassara shine ministan kiwon lafiyar al’umma. Ya kuma ce binkicen ya gano wasu basu da takardan bude makarata kuma suka je suka bude.
Binciken ya kuma gano yadda a ke fatali da tsarin jarabawar bai daya dake bada damar tantance daliban da suka cancanci samun diflomar kammala karatun likitanci.
Mun tuntubi shugabanin kungiyar mamallaka makarantun horar da jami’an kiwon lafiya masu zaman kansu amma sun bukaci mu ba su dama idan suka kammala wani taron da suke gudanarwa a yau litinin zasu kira mu a waya.
Da yake bayyana ra’ayinsa a game da matakin rufe wadanan makarantu wani jigo a kungiyar kwararrun likitoci ta SYMPHAMED Dr Habou Abdourahamane ya ce matakin ya yi dai dai a bisa la’akari da mahimmancin sha’anin kiwon lafiya a rayuwar dan adam.
A takardar da ya aika wa shugabanin makarantun da matakin gwamnatin ya rutsa da su ministan makarantun kimiya da na koyar da sana’oin hannu Kassoum Maman Moktar ya umurce su da su dakatar da karatu har zuwa lokacin da suka tabbatar sun cike ka’idodin koyar da sha’anin kiwon lafiya.
Saurare rahoton a sauti: