NIAMEY, NIGER - Da yake jawabi a zauren majalissar dokokin kasa a yayin zaman gabatar da kasafin 2023, Ministan kudin Niger Dr. Ahamed Djidoud, ya sanar cewa matsalolin da suka samo asali daga gardamar daminar shekarar 2021 inda aka yi asarar kashi 40 cikin 100 na amfanin gona da ya kamata a samu a wani lokaci da illolin annobar coronavirus ke ci gaba da tasiri a harkokin yau da kullum, da faduwar tattalin arziki a cikin gida da ma wanda duniya ta tsinci kanta ciki sanadiyar yakin da Rasha ta kaddamar a Ukraine, lamarin da ya haddasa hauhawar farashin ababen masarufi. Sannan duk da cewa an sami lafawar tashe tashen hankula a jihar Diffa da wani bangare na yankin gabar kogin Kwara, yanayin tsaro a kan iyakar kasashen 3 ya tabarbare, wadannan abubuwa sun haddasa cikas wajen aiwatar da kasafin 2022.
Djidoud ya kara da cewa a watanni 6 na farkon wannan shekara billion 1,192 da ‘yan kai na CFA ne suka shiga aljihun kasa daga cikin billion 2,908 na CFA da aka yi hasashen za a tattara, wato kashi 41 daga cikin 100 kenan, a yayin da a bangaren kudaden da ya kamata a kashe ba su fice kashi 36 daga cikin 100 na abin da aka kudirta ba.
CFA billion 3,245 ne gwamnatin ta kudiri aniyar kashewa a shekarar 2023 a cewar ministan a lokacin da yake gabatar da wannan kasafi a gaban ‘yan majalisa, a wannan karon galibin kudaden da ake bukata za a tattaro su ne daga cikin gida, inji shi, sabanin yadda a baya ake bai wa kudaden rance da na tallafin kasashen waje fifiko.
Jigo a kungiyar RNDD mai yaki da cin bashin kasashen waje Salissou Amadou, ya yaba da sabuwar alkiblar gwamnatin ta Nijer a sabon kasafin da aka gabatar wa majalisar dokokin kasa.
Asusun Lamuni na FMI ko kuma IMF da bankin duniya sun ayyana Nijer a sahun kasashen da zasu samu ci gaban tattalin arziki a shekarar 2023, lamarin da ake dangantawa da shirin da kasar ta sa gaba don fitar da man fetur dinta zuwa kasuwannin duniya ta hanyar bututun man da ake shimfidawa a yanzu haka daga matatar Damagaram zuwa tashar jirgin Ruwan Seme a jamhuriyar Benin.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma: