Yayin da zaben shekarar 2023 ke karatowa a Najeriya, ana iya cewa akwai manyan 'yan takarar shugaban kasa guda 4 daga jam’iyyu dabam daban da suka hada da APC, PDP, NNPP, da kuma jam’iyyar Labour. Masana harkokin siyasa sun yi hasashen cewa sai mai tsananin rabo da tarin magoya baya zai kai labari.