Iyalan fasinjojin jirgin ƙasan Kaduna da suka rage hannun yan bindiga sun mamaye hedkwatar ma'aikatar Sufuri ta ƙasa, Abuja
'yan uwan fasinjojin da aka sacen sun yi zaman dirshan din ne a ganban ma’aikatar sufuri da ke Abuja a Najeriya, bayan wani faifan bidiyon azabtar da yan’uwansu da 'yan ta’addan ke yi ya karade kafafen yanar gizo.
'Yan’uwan wadanda ke riken dai sun bukaci gwamnati ta kawo musu dauki ganin an kwashe sama da kwanaki 100 babu wani sahihin labari da zai tabbatar da kabutar da yan’uwan na su
Daya daga cikin mahaifiyar fasinjojin da 'yan ta’addar da su ka kai hari kan jirgin kasa na Abuja zuwa kaduna kenan ta yi magana cikin tashin hankali da fargabar halin da ta ga danta ke ciki bayan bidiyon da 'yan ta’addar suka sake sama da sa’o’i 24 da suka gabata.
Bidiyon dai ya nuna sauran mutanen da ke tsare a hannu, su na cikin damuwa inda gungun ‘yan ta’addar ke amfani da bulala su na dukar maza da ga cikinsu. A halin da ake ciki dai an kwashe sama da watanni hudu da aka kai wannan mummunan hari kan jirgin kasa.
Idan an tuna, 'yan ta'addar sun sace Fasinjoji sama da 60, kuma aƙalla 20 daga ciki sun kuɓuta bayan biyan kudin fansa har Naira miliyan N100m a kan kowane mutun. Zahra Aliyu, wata yar’uwar daya daga cikin fasinjojin da suka saura a hannu yan’ta’addar ta bayyana takaicinta.
'Yan uwan fasinjojin dai sun yi zaman dirshan a gaban ma'aikatar sufuri inda suka hana ma’aikatan shiga ofishinsu har sai sun samu gamsasshshen bayani daga hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa.
Wasu daga cikin masu zaman dirshan din na ɗauke da allunan sako da aka yi rubutu na kira ga gwamnati kan a kawo musu dauki tare da kuɓutar musu da 'yan uwan su, sai dai har ya’ zuwa rubuta wannan rahoto babu wani da ya tamka musu daga ma’aikatar.
Shugaba Buhari ya sha nanata cewa ya ba da umarni ga hukumomin tsaro da su kuɓutar da fasinjojin, kuma yana da tabbacin jami’an su na yin duk abun da ya dace don ceto su.
Sai dai cikin sanarwar da mai taimaka ma shugaban kan al’amuran yada labarai, Malam Garba Shehu ya ce gwamnati ba za ta firgita don barazanar ‘yan ta’addar ba, domin abun da su ka yi ba sabon abu ba ne a duniya.
Batun da masanin tsaro a kasar, Manjo Yaya Shinku mai riyata ya ce hakan na nuni da cewa gwamnatin ta gaza.
Saurari rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim: