Yanayin da ya jawo mata asarar kusan kaso 81.46 na Jarinta dake waje, inda ta yi asasar kudi har Dalar Amurka $6.91bn daga Jarinta da ya kai Dala biliyan $8.4 zuwa abinda bai fi Dalar Amurka 1.57bn ba.
Hakan kuwa ya faru ne daga kashin farko na shekarar 2019 zuwa kashin farko na shekarar 2022.
Hukumar Kididdigar ta Najeriya dai wato National Bureau of Statistic ta bayyana cewa tun daga kashin farkon na shekarar 2019 zuwa kashin farko na shekarar 2022 ne kasar ta shiga cikin wannan mawuyacin halin, duk da an dangata wannan lamarin da matsalar cutar covid 19 da ya durkushe al’amura da dama a duniya da kuma yakin dake tsakanin kasar Rasha da Ukraine ya haifar.
Muhammad Yusuf Lere na Cibiyar inganta harkokin Kasuwanci da zuba jari da Masana’antu a Najeriya yayi bayani cewa rashin tsaro da karancin wutar lantarki ne suka taimaka wajen hana zuwan masu zuba jarin a Najeriya.
Kamar yadda rahotan ya bayyana a cikin shekarun uku na 2019 zuwa 2022, fannin zuba jari ta fuskar hada-hadar bankuna ne kawai ke motsawa inda ake samun shige da ficen kudade, Amma duk da haka masanin tattalin Arziki Kasim Kurfi ya ce akwai sauran runa a kaba.
Sai dai a cewar Ministan Ayyukan Noma da raya kasa, Dakta Muhammad Mahmud Abubakar duk da wadannan matsaloli da ke kasa, gwamnati kasar ta dauki matakai don shawo kan wannan yanayi.
Ko da yake dai babbban bankin Najeriya ya bayyana cewa rashin kyawun yanayin zuba jari na cikin gida na yin tasiri ga jarin da ke shigowa kasar.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: