Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Izala Ta Aurar Da Mata 20 A Abuja


Bukin auren 'yan mata marayu a Abuja
Bukin auren 'yan mata marayu a Abuja

Kungiyar izala reshen babban birnin tarrayar Najeriya Abuja ta dauki nauyin aurar da yan’mata marayu marasa galihu 20 tare da ba su tallafin kudi da sana'oin yi domin dogaro da kai .

A wani yunkuri na kawo sassauci ga rayuwar mata da kananan yara musamman marayu da a halin yanzu matsalolin tsaro da talauci ya tilasta wa yin gararamba a kan tinunan Najeriya, an soma samun sauki ta fannin tallafi daga daidaikun kungiyoyi inda kungiyar izala ta bi sahu wajen aurar da wasu mata marayu marasa gata su 20 tare da basu tallafi na kudi da sama musu sana'ar yi.

Duk da cewa akwai dimbin kalubalen da ma’aurata ka iya fuskanta a zamnatakewarsu, Haj.Rabi Muhammad mai fafutukar kare hakkin mata kana shugaban kungiyar Domin Marayu ta ce ba su yi kasa a gwiwa ba wajen fadakar da amaren

Bukin auren 'yan mata marayu a Abuja
Bukin auren 'yan mata marayu a Abuja

Tabarbarewar tsaro, daya ne daga cikin matsalolin da Najeriya ke fama da shi, lamarin dake tilastawa mata da yara rayuwa a kan tituna kara zube, duk da kasancewarsu masu rauni, dalilin da ya sa ake cigaba da jan hakula ga masu hannu da shuni da gwamnati za su shigo wajen rage nauyin wallahalu da marayu marasa galihu ke fuskata wajen agaza musu.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG