A baya dai shugaban Najeriya kuma shugaban jam’iyyar APC, Muhammadu Buhari, ya bayar da umanin a mayarwa da dukkan yan takarar da suka sayi fam, daga bisani kuma suka ajiye takararsu don baiwa jam’iyya damar zaben shugaba ta hanyar sulhu kudadensu.
Jam’iyyar APC ta sayar da fam din takarar neman shugabancinta kan Naira miliyan 20, inda a gabannin yin zaben, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci a janyewa Sanata Abdullahi Adamu, wanda da ya samu shugabancin ta hanyar daidaitawa.
Mafi karancin shekaru daga ‘yan takarar Muhammad Sa’idu Etsu ya ce shiru su ke ji wai malam ya ci shirwa, amma har yanzu ya ce suna zuba ido suna jira. Ya kuma nuna rashin jin dadinsa da rashin sanin za a zabi shugaba ta hanyar sulhu, wanda da basu saye fam da kudinsu ba.
A martanin jam’iyyar ta bakin dan kwamitin gudanarwarta Dattuwa Ali Kumo, a yanzu haka an kafa kwamitin da ke aikin duba wadanda su ka cancanta da samun kudin.
Faruwar wannan al’amari ya sa sashen Hausa duba bangaren babbar jam’iyyar adawa ko itama ta na fuskantar irin wannan yanayi na sulhuntawa da neman mayarwa ‘yan takara kudadensu.
Yusuf Dingyadi mai taimakawa shugaban jam’iyyar PDP Iyorchia Ayu kan labaru, ya ce tsarin jam’iyyarsu ya sha bamban da na APC kuma umurnin shugaba Buhari bai shafe su ba.
Duk da jam’iyyu a wannan karo sun caji kudi na sayar da fom a dukkan matakai, amma na APC shi ya fi tsada a tarihi musamman na takarar shugaban kasa da ya kai Naira miliyan 100 ko saya ko bari.
Manyan jam’iyyun Najeriya sun caji kudaden sayar da fam na takara a dukkan matakan jam’iyya, amma kudin da jam’iyyar APC ta saka ya fi tsada a tarihi musamman na takarar shugaban kasa da ya kai Naira miliyan 100 ko saya ko bari.
Domin Karin bayani saurari cikakken rahotan Shamsiyya Hamza Ibrahim: