ABUJA, NIGERIA - Ana sa ran shirin zai kebe wuri na musamman da za’a yi noma da zai samar da abinci ga dabbobi da ake yawo da su.
An kaddamar da wannan shiri ne a filin kiwo na Paikon Kore dake Gwagwalada a babban birnin tarayya na Abuja a matsayin daya daga cikin matakai da dama da gwamnatin tarayya Najeriya ta mai da hankali akai.
Manufar wannan matakin shi ne a dakile yawan tashe-tashen hankula dake tsakanin makiyaya da manoma da ya ki ci ya ki cinyewa a wasu sassan kasar da kuma inganta dorewar abinci, tattalin arzikin kasa, da kuma fitar da kayayyakin kiwo zuwa kasashen waje.
Manufar ci gaban wannan tsari dai shi ne samar da yanayin da ya dace don samun abinci da zai kawo karshen tsarin kiwon gargajiya na yawon da makiyaya a Najeriyar ke yi a tsakanin yankunan arewaci da kudancin kasar da kuma mahimmi samun rufin asiri a cewar Muhammad Ali baba wanda shi ne shugaban kungiyar ta masu noman ciyawar dabbobi a Najeriya.
Shi ma Dakta Iyusa Mohammad Ishayaku dake aiki da ma’aikatar dabbobi ta NAPRE dake jami’ar Ahmadu Bello a zaria ya yi kari da cewa hakan zai taimaka so sai.
Sai dai al’ummar yankin Paikon kore na karamar hukumar Gwagwalada da aka fara wannan tsari a wajensu sun bayyana kokensu da zargin gwamnati da kwace musu gonaki.
Shugaban kungiyar manoma masu shuka ciyawa a Najeriya mai martaba Sarkin Muri na jihar Taraba Alhaji Abbas Tafida ya ce sai da hadin kai za’a samu fahimta don cin moriyar wannan sabon tsari.
An dai ayyana duk ranar 28 ga watan Yuni na ko wacce shekara a matsayin ranar tuni da wannan sashi da zai himmatu wajen wayar da kan al’umma da manoma da horar da su dabarun noman kiwo iri-iri.
Saurari rahoto cikin sauti daga Shamsiyya Hamza Ibrahim: