Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Zata Hada Hannu Da China Wajen Inganta Noma Ta Hanyar Amfani Da Sabuwar Fasaha Ta JUNCAO

Najeriya Zata Hannu Da CHina Wajen Inganta Noma Ta Hanyar Amfani Da Sabuwar Fasaha Ta JUNCAO
Najeriya Zata Hannu Da CHina Wajen Inganta Noma Ta Hanyar Amfani Da Sabuwar Fasaha Ta JUNCAO

Gwamnatin Najeriya za ta hada hannu da kasar China wajen amfani da sabuwar fasaha ta ciyawar da ake kira JUNCAO daga kasar China don taimaka wa fannin noma, duba da yadda kwararowar hamada da sauyin yanayi ke jefa miliyoyin jama'a cikin talauci da kuma illata muhalli,

ABUJA, NIGERIA - Hakan zai tabbatar da cewa manoma sun rungumi dasa sabon nau'in ciyawar da ke hana zaizayar kasa da kuma samar da ayyukan yi ga dubbun matasa a Najeriya da inganta tattalin arzikin kasar.

Gwamnatin Najeriya ta ce a shirye take ta hada hannu da gwamnatin china kan fasaharta ta ciyawar JUNCAO domin samun wadatar abinci a kasar, matsalar da akasari ake dangantawa da sauyin yanayi.

Najeriya Zata Hannu Da CHina Wajen Inganta Noma Ta Hanyar Amfani Da Sabuwar Fasaha Ta JUNCAO
Najeriya Zata Hannu Da CHina Wajen Inganta Noma Ta Hanyar Amfani Da Sabuwar Fasaha Ta JUNCAO

Darakta a ma’aikatar noma da raya karkara, wanda ya wakilci babban Ministan ma’aikatar a wajen taron kaddamar da fasahar a Najeriya, Injiniya Abdullahi Garba Abubakar ya bayyana alfanun fasahar ga Najeriya a wannan lokaci.

Sashen Tattalin Arziki da Zamantakewa na Majalisar Dinkin Duniya (UNDESA) tare da cibiyar dake samar da bincike ta fasahar Juncao a jami'ar aikin gona da gandun daji ta Fujian (FAFU) na kasar China karkashin Gidauniyar wanzar da zaman lafiya da ci gaba ta majalisar dinkin duniya ne suka gabatar da wannan shiri ga Najeriya da ake yi wa take da "Haɓaka ƙarfin ƙasashe masu tasowa don cimma nasarar noma mai ɗorewa” ta hanyar musayar fasahar Juncao don kawar da talauci da haɓaka ayyukan yi masu inganci.

Najeriya Zata Hannu Da CHina Wajen Inganta Noma Ta Hanyar Amfani Da Sabuwar Fasaha Ta JUNCAO
Najeriya Zata Hannu Da CHina Wajen Inganta Noma Ta Hanyar Amfani Da Sabuwar Fasaha Ta JUNCAO

Jakadan kasar China a Najeriya, H. E Cui Jianchun, ya bayyana cewa asalin wannan fasaha ta JUNCAO an yi ta ne don taimaka wa dan adam da muhallinsa,

Ya ce “na yi farin cikin bayyana wannan fasaha ta kasar China ga Najeriya kuma daya daga cikin ayyukan da na sa a gaba a kasar shi ne tabbatar da cewar an samu wata cibiya a Abuja ta fasahar JUNCAO, don zai sa a samu cikkaken alfanun wannan fasaha ta hanyar samar da abinci, ayyukan yi, rage rikice rikice tsakanin makiyaya da manoma da dai sauransu, ina kuma fatan nan gaba Najeriya zata samar da irin wannan fasaha ga sauran kasashen duniya”.

Najeriya Zata Hannu Da CHina Wajen Inganta Noma Ta Hanyar Amfani Da Sabuwar Fasaha Ta JUNCAO
Najeriya Zata Hannu Da CHina Wajen Inganta Noma Ta Hanyar Amfani Da Sabuwar Fasaha Ta JUNCAO

Alfanun wannan fasaha na da matukar yawa ta fuskar tattalin arzikin da al’umma ke bukata ta hanyar inganta ayyukan noma da rage zaizayar kasa da kwararowar Hamada.

Ya zuwa yanzu dai sama da kasashe 100 ke amfani da wannan fasaha kuma a Najeriya tuni jihohi irin su Nassarawa, Benue Plateau, Anambra, Adamawa, Rivers da Bauchi suka rungumi wannan fasaha ta JUNCAO.

Saurari rahoto cikin sauti daga Shamsiyya Hamza Ibrahim:

Najeriya Zata Hannu Da CHina Wajen Inganta Noma Ta Hanyar Amfani Da Sabuwar Fasaha Ta JUNCAO.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00

XS
SM
MD
LG