ABUJA, NIGERIA - Tuni dai aka kammala zaben fidda gwani a Najeriya inda manyan jam’iyyun siyasar Kasar suka gabatar da masu tsaya musu takarar neman shugabanci a babban zaben da ke tafe na shekarar 2023.
Jam'iyyar APC mai mulki ta tsayar da Sanata Bola Ahmad Tinubu a matsayin jagoranta, yayin da jam’iyyar PDP ta tsayar da Alhaji Atiku Abubakar, ita kuma jam’iyyar NNPP ta tsayar da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, sai kuma tsohon gwamnan jihar Anambra Peter Obi da jam’iyyar Labour ta tsaida.
An yi itifakin zaben zai yi matukar jan hankali saboda jam'iyyun hamayya da ke kokarin hankade jam'iyyar APC daga karagar mulki.
To ko wanne kalubale ne ’yan takarar kujerar shugaban Kasa a Najeriya ka iya fuskanta? La’akari da cewa ba wannan ne karon farko da 'yan takarar suka taba tsayawa takarar neman shugabancin kasar ba, in banda Peter Obi.
Masanin harkokin siyasa a Najeriya Dakta Abubakar Kyari, ya ce babban kalubalen da ke gaban 'yan takarar shi ne su nemi goyon baya da kuma rarrashin wadanda aka kada a zaben don a tafi tare a kuma kaucewa samun matsala a gaba.
Shi ma masanin kimiyar siyasa a kasar Dakta Faruk BB Faruk ya ce jam’iyyar NNPP da Labour ka iya zame wa jam’iyyu biyu da suka yi fice a kasar barazana, wato APC da PDP.
Tuni dai ‘yan takarar manyan jam’iyyun suka soma gudanar da ziyarce-ziyarce don jan hankalin masu ruwa da tsaki da samun hadin kai musamman daga wadanda suka janye ko aka kada su a wajen neman takarar.
Daya daga cikin manyan magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari kuma sakataren yada labarai a kungiyar da ke bada goyon baya ga shugaban kasa, Dr. Muhammad Kailani, ya bayyana kwarin gwiwa kan cewa APC ce zata samu nasara a babban zaben saboda goyon bayan da suke samu.
Shi ko Honorabul Aliyu Bello cewa ya yi ko shakka babu jam'iyyar PDP ce zata yi nasara a zaben mai zuwa, ya kara da cewa yanzu yanayi ya canza mutane sun gaji da yaudara da ake yi musu.
Aiki na farko da ke gaban 'yan takarar shi ne yin manyan tsare tsaren da zasu taimaka wajen tafiyar da yakin neman zabe da zai karade kasar, lungu da sako.
Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim.