ABUJA, NIGERIA - Masu safarar mutanen suna amfani ne da sabbin hanyoyin ta kafafen sada sumunta don yaudarar mutane zuwa wasu kasasen waje da sunan za a ba su rayuwa mai kyau.
Wannan sabuwar dabara na zuwa ne sakamokon matsin lamba da gwamnatin Najeriya ke yi a zahiri ga masu aikata irin wannan mummunar dabi’a
Hukumar NAPTIP dai ta ce miyagun irin sun canja salo da dabarun yaudarar mutanen da ake fataucinsu zuwa wasu kasashe a zahirance saboda kama su da jami’an tsaro ke yi a Najeriya, a yanzu haka dai sun karade kafofin sadarwa na yanar gizo a faddin kasar inda suke janyo hankalin masu fadawa tarkonsu.
Akasarin lokuta matasa ne suka fi fadawa tarkon miyagun irin dake amfani da sunan ba su aiki ko samun karatu, da damar yin wasannin motsa jiki na karya a kasashen waje. Wata matashiya da ta shaida mana haka, Fauziya Munir, na cikin matasan da suka fada tarkon wadannnan mutane ta yanar gizo amma ta sha da kyar.
Haka kuma kwararre kan harkar sadarwa a Najeriya Yusufdeen A. Yusuf ya yi mana karin haske game da wannan sabuwar hanya da masu fataucin mutanen ke amfani da shi, kamar yadda za a ji a sauti.
Babban jami’i a kungiyar dake fafutukar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa a Najeriya wato Amnesty International, Awwal Musa Rafsanjani, ya ce wannan lamari ne da ke bukatar a ci gaba da wayar wa da al’umma kawunansu.
Fataucin mutane zuwa kasashen Turai da sauran kasashen duniya ya zama babban annoba wanda mafi yawan alkawuran da ake yi wa mutane bashi suke taddawa ba, hasali ma sai dai ya jefa rayukansu cikin hatsari.
Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim: