Ana ci gaba da kirga kuri'u a jihohin da ke gabar Amurka ta Gabas da duk fadin kasar, bayan da Amurkawa suka yanke shawarar ko za su bai wa shugaban kasa Donald Trump na jam’iyyar Republican wani wa'adin shekaru hudu, ko kuma su mika Fadar White House ga dan takarar jam’iyyar Democrat Joe Biden.
Jama'a a fadin Amurka su na kada kuri'a a ranar karshe ta zaben shugaban kasar na 2020. Tuni miliyoyin 'yan kasar suka kada kuri'unsu da wuri kafin ranar zaben, Talata.
Shugaban Amurka Donald Trump da abokin kaeawarsa na jam'iyyar Democrat, tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden, sun ziyarci jihohin da ake yiwa lakabi da fagen daga jiya Lahadi, don karawa magoya bayansu karfin gwiwa.
Gwamnatin jihar Kogi ta ce ta tafka asarar miliyoyin Naira sakamakon wawashe kayan abinci da kaddarorin gwamnatin jihar da aka yi a ma’ajiya.
Ofishin jakadancin Amurka a jamhuriyar Nijer ya bukaci mutanen da suka sace wani Ba-Amurke a ranar Talata a garin Masallata dake yammacin birnin Konni, su gaggauta sakinsa.
Wasu yan Najeriya sun daura alhakin karancin man fetur da zanga-zangar gama gari ta nema kawo karshen ‘yan sandan yaki da ‘yan fashi #EndSARS a kasar.
Yan takarar Shugaban kasar Amurka sun bayyana abinda ya banbanta su da kuma yadda za su tinkari muhimman matsalolin da suka tsonewa Amurkawa Ido
Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila ya yi barazanar cewa ba zai amince da kasafin kudin shekara 2021 ba sai shugaba Mohammadu Buhari, ya dauki wasu kwararan matakai da za su kawo karshen zanga-zangar da a yanzu haka ke ci gaba a fadin kasar.
Gwamnatin jihar Pilato ta saka dokar hana fita na tsawon sa’o’i 24 a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta kudu, har sai yadda hali ya yi.
Kwamitin shugaban kasar Najeriya dake gudanar da bincike kan annobar cutar Coronavirus a kasar, ya yi hasashen cewa nan da mako biyu masu zuwa za a sake samun yaduwar cutar a fadin kasar, ganin yadda masu zanga-zanga ke bijirewa ka’idojin hukumomin lafiya na kare kai daga kamuwa daga cutar.
Jiya Lahadi shugaban Amurka Donald Trump da mai kalubalantarsa na jam’iyyar Democrat Joe Biden suka yi zawarcin masu jefa kuri’ar farko a jihohin da ake fafatawa jihar Nevada da North Carolina, yayin da muhawarar karshe ta shugaban kasa ke karatowa a wannan makon.
Fitaccen mai wakar gambara na Amurka Kenye West, ya shiga jerin shahararrun mutane a fadin duniya dake goyon bayan gagarumar zanga-zangar kawo karshen cin zarafin ‘yan sanda a Najeriya.
Malaman makarantun firamare a Abuja sun kauracewa aikin koyarwa tare da tura dalibai gida.
Babban Sufeto Janar din ‘yan sandan Najeriya Muhammad Adamu, ya soke runduna ta musamman da ke yaki da masu fashi da makami wacce ake kira SARS a takaice.
A kalla malaman makaranta 3,000 a kasar Kamaru sun ki amincewa da tayin da rundunar sojin kasar ta yi musu na jigilarsu zuwa makarantunsu a yankin da masu amfani da harshen turanci da ake tashin hankali.
Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ware duk ranar 11 ga watan Oktoba domin domin nazari kan ci gaba da kuma kalubalen da suke fuskanta a fadin duniya, taken wannan shekarar shine Muryata Makomarmu Daidai.”
Biyo bayan zanga-zangar da ‘yan Najeriya ke fitowa suna gudanarwa a wasu manyan biranen kasar, domin neman kawo karshen cin zarafin ‘yan sanda ga fararen hula. Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa sun gana da Sufeto Janar na ‘yan Sanda.
Shugabar hukumar bunkasa zuba jari a Najeriya (NIPC) Yewande Sadiku, ta ba da tabbacin aiki da hukumar kasuwanci ta jiragen ruwa wajen samun rage haraji don kara janyo hankalin masu zuba jari su ci gaba da shigowa Najeriya.
Kungiyar farar hula dake lura da ci gaba da kuma kare hakkin al’umma mai suna Centre for Advancement of Civil Liberties and Development, ta gudanar da zanga-zanga ta hanyar amfani da hotunan balan-balan ta yanar gizo, domin nuna adawa da salon mulki da kuma manufofin gwamnatin Najeriya.
Majalisar Limaman birnin Abuja ta gudanar da gagarumin taro don karfafa Limamai gwiwa su ci gaba da tsayawa kan gaskiya tare da gujewa marawa wani bangaren siyasa baya.
Domin Kari