Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Ba Sufeton ‘Yan Sanda Umarnin Kawo Karshen Cin Zarafin Jama'a


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Da Mataimakinsa Osinbajo Sun Gana Da Sifeton 'Yan Sanda.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Da Mataimakinsa Osinbajo Sun Gana Da Sifeton 'Yan Sanda.

Biyo bayan zanga-zangar da ‘yan Najeriya ke fitowa suna gudanarwa a wasu manyan biranen kasar, domin neman kawo karshen cin zarafin ‘yan sanda ga fararen hula. Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa sun gana da Sufeto Janar na ‘yan Sanda.

Wannan shi ne karo na biyu cikin kwana guda da shugaba Buhari ya gana da Sufeto Janar na ‘yan Sanda IGP Mohammed Adamu, domin neman bakin zaren warware matsalar da ke damun ‘yan Najeriya game da cin zarafi da ke karuwa a fadin kasar.

A wani sako da ya wallafa a shifinsa na twitter, shugaba Buhari ya ce “Na sake ganawa da sufeto janar na ‘yan sanda a yau. Kudurinmu na sake fasalin hukumar ‘yan sanda babu shakka cikinsa. Ina samun bayanai akai-akai kan yunkurin da ake na samar da sauyin da zai kawo karshen cin zarafin da ‘yan sanda su ke yi da rashi da’a.”

Shugaban ya ci gaba da cewa yanzu haka ya bai wa suifeton ‘yan sanda umarnin ya shawo kan wannan matsala da ta addabi ‘yan Najeriya, tare kuma da tabbatar da duk jami’an da aka samu da cin zarafi ya fuskanci shari’a.

An gudanar da zanga-zanga a wajen ginin Majalisar jihar Lagos har zuwa cikin dare ranar Alhamis, masu zanga-zangar dauke da kwalaye masu rubutu suna fadin ‘End SARS’ wato a kawo karshen sashen hana fashi da makami.

Cin zarafi da 'yan sanda ke yi a fadin Najeriya abu ne da ya zama ruwan dare, wanda ya hada da kafa shingaye domin bincikar ababen hawa tare da karbar kudaden a hannun direbobi, idan mutuum bai bayar ba ya fuskanci cin zarafi da ya hada har da dukan tsiya.

Tun ranar Lahadi ne rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da dakatar da ayyukan wasu rundunonin ‘yan sandan da suka hada da na yaki da fashi da makami na tarayya (SARS) da dabaru na musamman (STS) da rundunar kai agaji ta Leken Asiri (IRT) daga ci gaba da gudanar da ayyukan sintiri da kafa shigayen binciken ababen hawa da sauran ayyukan tsaro akan manyan hanyoyi.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG