Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Da Biden Sun Karfafa Gwiwar Magoya Bayansu A Jiya Lahadi


Trump da Biden
Trump da Biden

Shugaban Amurka Donald Trump da abokin kaeawarsa na jam'iyyar Democrat, tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden, sun ziyarci jihohin da ake yiwa lakabi da fagen daga jiya Lahadi, don karawa magoya bayansu karfin gwiwa.

Ziyarar 'yan takarar zaben shugaban kasar na zuwa ne kwanaki biyu gabanin zaben kasa na gobe Talata don neman wa’adin shekaru hudu a Fadar White House.

Trump ya fara ziyarar ta sa ta zuwa jihohi biyar da yankin Macomb na jihar Michigan, jihar da ba zato ba tsammani ya sami nasara da kuri’u 11,000 a zaben 2016 kan Hillary Clinton ta jam’iyyar Democrats.

Yau Litinin Trump zai halarci wasu taruka biyu a Michigan, ciki har da maimaita yakin neman zabensa na karshe daga shekaru hudu da suka gabata, a wani taron gangami da za a yi cikin dare a birnin Grand Rapids, dake da mafi akasarin masu ra'ayin mazan jiya a yammacin jihar ta Michigan.

Amma zabukan jin ra’ayin masu zabe na baya-bayanan na nuna cewa Biden ne ke da fifiko a kan Trump a jihohin Michigan da Wisconsin, sai kuma mai-yiwuwa a Pennsylvania, jihohi ukun da a baya jam’iyyar Democrats suke zaba, amma Trump ya yi nasara shekaru hudu da suka gabata amma Biden na fatan kwatowa.

Dukansu Trump da Biden sun sha ziyartar dukkanin jihohin uku, inda Trump ya gudanar da taruka hudu a Pennsylvania a ranar Asabar, shi kuma Biden ya gudanar da taruka biyu a can jiya Lahadi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG