Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Malaman Makaranta A Kamaru Na Kaucewa Yankin 'Yan Aware


A kalla malaman makaranta 3,000 a kasar Kamaru sun ki amincewa da tayin da rundunar sojin kasar ta yi musu na jigilarsu zuwa makarantunsu a yankin da masu amfani da harshen turanci da ake tashin hankali.

Malaman wadanda suka gujewa hare-haren ‘yan aware da sace-sace da kuma mamayar makarantunsu a yankin na masu amfani da ingilishi, sunce basu da tabbacin kare rayukansu yayin da wasu mayakan ‘yan aware ke ci gaba da barazanar kashe malaman da daliban da suka je makaranta.

Malamin makarantar firamare mai shekaru 47, Fru Issac ya bayyana cewa yaki karbar tayin da sojojin Kamaru na daukarsa zuwa makarantar dake ‘yankin. Duk da haka, Fru ya ce abokan aikinsa shida sun amince sojoji su rika daukarsu daga garin Bamenda zuwa Ndop dake Arewa maso yammacin yankin masu amfnai da harshen ingilishi.

Ya ce “Hukumomi yanzu suke daukar malamai da basa iya zuwa wuraren aikinsu a motocin sulke. Amma tambaya anan itace, idan aka dauke su zuwa makarantun, yaya malamai za su yi idan babu wadannan motocin sulken?.

Sojojin Kamaru sunce suna cikin shirin ko ta kwana tun ranar 5 ga watan Oktoba, lokacin da sabuwar shekarar karatu ta 2020 zuwa 2021 za ta fara, domin su dauki malaman da dalibai da kuma ma’aikatan makarantun daga garuruwa da kauyukansu.

Sai dai, ma’aikatun dake kula da makarantun firamare da sakandare sunce sama da malamai 3,000 basu je wurin aikinsu ba a makon da ya gabata.

Kasar Kamaru ta sanar da bude makarantu 140 cikin 500 da mayakan suka rufe cikin shekaru hudu da suka gabata , da kusan dalibai 30,000 da suka je makarantun.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG