Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Da Biden Sun Kara Kaimi A Wurin Kempe A Jiya Lahadi


Trump da Biden.
Trump da Biden.

Jiya Lahadi shugaban Amurka Donald Trump da mai kalubalantarsa na jam’iyyar Democrat Joe Biden suka yi zawarcin masu jefa kuri’ar farko a jihohin da ake fafatawa jihar Nevada da North Carolina, yayin da muhawarar karshe ta shugaban kasa ke karatowa a wannan makon.

A kalla Amurkawa miliyan 27.7 suka kada kuri’unsu ta gidan waya ko ta hanyar zuwa da kansu gabannin ranar 3 ga watan Nuwamba ranar zabe, a cewar cibiyar dake kula da harkokin zabe dake jami’ar Florida. Samun yawan adadin masu jefa kuri’a da wuri ya faru ne game da damuwar da ake da ita kan cunkoso a rumfunan zabe a yayinda ake fama da annobar coronavirus.

A jihar North Carolina, ‘daya daga cikin fagen fafatawar, inda mutane miliyan 1.4 ko kashi 20 cikin 100 na wadanda suka yi rijistar zabe suka kada kuri’unsu ya zuwa jiya Lahadi, Biden ya yi kira ga mazauna jihar da su je su kada kuri’a da zarar sun sami sukuni.

Biden ya caccaki Trump game da wasu kalamai da ya yi a karshen mako cewa Amurka ta fara samun daidaitar al’amura a wannan annobar coronavirus, Biden na mai cewa sababbin kamuwa da a fadin kasar na kara haurawa ne a cikin wannan wata.

Mai dafawa Biden baya a takarar shugaban kasa, Sanata Kamala Harris ta fasa halartan gangamin yakin neman zaben na karshe mako a wani matakin kiyayewa bayan an tabbatar da wani hadiminta ya kamu da COVID-19. Zata koma yakin neman zaben ne a yau Litinin a wata ziyara zuwa jihar Florida domin fara zaben zuwa da kai na wuri a jihar.

Gwaji a jiya Lahadi ya tabbatar da Harris bata kamu da coronavirus ba. Inji kwamitin yakin neman zaben.

Shugaban kasa da bai saba zuwa coci ba amma kuma yake da goyon bayan masu wa’azin addinin Krista, saboda kyamarsa da barar da ciki da kuma nada alkalai masu ra’ayin mazan jiya, ya fara wuninsa ne da zuwa coci a mujami’ar International Church a Las Vegas.

Trump da ya kamu da cutar coronavirus a kwanan nan, bai saka abin rufe baki da hanci ba saboda a wurin ibadar dake rufe.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG