An dai fara fuskantar karancin Man Fetur a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, da wasu birane makwabta tun karshen makon da ya gabata inda wasu ‘yan kasar ma suka daura alhakin hakan ga zanga-zangar #EndSARS.
Mazaunin birnin Abuja Mallam Abdulkadir, ya bayyanawa Muryar Amurka yadda ya bi dogon layi da ya fada sakamakon karancin man fetur. Inda ya ce bayan kwashe tsawon lokaci akan layi, har sai da ya bayar da Naira dubu daya kafin a bashi damar shiga gidan man.
Shi kuma mai sana’ar bunburutu Muhammad Rabiu, ya alakanta rashin wadatar Man da zanga-zangar gama gari ta #EndSARS, yana cewa ganin yadda gwamnati ba ta kara kudin Mai ba hakan yana nufin babu hanyoyin da za a dauko Mai domin dakonsa ga wuraren da ake bukata.
Daya daga cikin ma’aikatan gidan man Azman a unguwar Area 11, Aliyu Muhammad, ya danganta karancin man da ake fuskanta da cewa ganin yadda a wasu yankunan Najeriya aka yi kone-kone, masu dakon Mai suna tsoron fitowa.
Mazaunan birnin Abuja dai na bin dogayen layuka kafin su samu damar cika tankunan su, inda ‘yan bunburutu ke sayar da litar Man Fetur hudu daga Naira 1000 zuwa dubu 1,200.
An dai fara zanga-zangar lumana ta #EndSARS ne a ranar 8 ga wannan watan da muke ciki, lamarin da ya rikide zuwa tarzoma daga bisani har ya kai ga afkawa runbunan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu da wasu batagari ke yi a sassan kasar daban-daban.
Domin karin bayani saurari rahotan Halima Abdulra’uf.
Facebook Forum