Zanga-zangar wacce aka yi wa taken “har yanzu ba a samu yanci ba” a cewar kungiyar duk da shekaru 60 da samun yancin kan Najeriya, har yanzu akwai rashin ci gaba da rashin shugabanci na gari.
Kungiyar dai ta fi mayar da hankali ne akan abubuwa biyar da ke ciwa al’ummar Najeriya tuwo a kwarya, wadanda suka hada da karin farashin kudin Man Fetur da na wutar lantarki, sai kuma dokar da ke duba ayyukan kamfanoni a kasar da kuma dokar kalaman nuna kiyyaya da ta kafofin shafukan sada zumunta.
Da yake zantawa da manema labaru dan fafutuka kuma dan gwagwarmaya a kungiyar Raphael Adebayo, ya ce manufarsu ita ce bayyana yadda al’amura suka tabarbare a kasar, wajen ta hanyar amfani da hotunan balan-balan masu launi daban daban dake nuna tutar Najeriya, kuma za su yi zanga zangar a kalla wurare 10 dake garin Abuja da kuma wurare 20 a fadin kasar.
Kungiyar dai ta bayyana cewa ta na so ta share shekaru 60 da kasar ta bata don samar da wani sabon yanayi duba da cewa wadanda ke rike da madafun iko sun gaza.
Domin karin bayani saurari rahotan Shamsiyya Hamza Ibrahim.
Facebook Forum