A karo na biyu an dakatar da taron manema labarai da gamayyar kungiyoyin Arewa (CNG) ta shirya a garin Kaduna, inda aka jibge jami’an tsaro tare da kame wasu shugabannin kungiyar.
Kungiyar Miyetti Allah ta gargadi ‘ya‘yanta da kar su dauki wani matakin ramuwa, game da harin da aka kai kan Fulani a garin Kurmin Bi na karamar hukumar Zangon Kataf.
Hukumar tsaron farin kaya ta DSS a Najeriya ta bankado wani yunkuri da wasu kungiyoyi ke yi, na tayar da rikicin kabilanci da na addini a kasar, ta hanyar kalaman tunzuri da raba kan al’umma.
Jam’iyyun da suka zo na uku da hudu a zagayen farko na babban zaben shugaban kasa a jamhuriyar Nijar, sun bada sanarwar hada kai tare da mara wa dan takarar jam’iyyar PNDS mai mulki baya.
An fara zurfafa bincike akan asalin kwayar cutar coronavirus a kasar China.
An bukaci sojojin da suka yi juyin Mulki, da su yi bayani mai gamsarwa, akan dalilin juyin mulkin.
Lamarin tsaro na ci gaba da tabarbarewa a daidai lokacin da hare-haren ‘yan ta’adda da masu satar mutane domin kudin fansa ke addabar wasu yankuna na jihar Kaduna.
Yayin da kowace nahiya a duniya ke bayyana irin matakan da ta ke daukawa wajen yaki da mugunyar cutar nan ta corona, Afurka ta ce ita ma ta himmantu ga wadata mutanenta da rigakafin cutar
A daidai lokacin da manyan kasashen duniya suka fara samar da allurar rigakafin cutar coronavirus, shugaban kasar Tanzania na tababa kan ingancin rigakafin.
Shugaban Hukumar Kula da Kafafen Yada Labarai ta Amurka, USAGM ya sauka da yammacin jiya Laraba bisa bukatar gwamnatin Shugaba Joe Biden, jim kadan bayan da Biden ya hau mulki.
A karon farko cikin shekaru sama da goma jam'iyyar Democrat ta Amurka ta samu rinjaye a dukkan Majalisun Amurka.
Sabon shugaban Amurka ya soke dokokin dake hana ‘yan wasu kasashen musulmai da wasu kasashen Afirka shiga Amurka.
Filin Ciki Da Gaskiya na wannan makon ya ci gaba da duba batun korafin jama'a a Kanon dabo, kan yunkurin gwamnatin jihar na raba wasu filaye ko wurare masu muhimmanci ga daidaikun mutane da wasu ke ganin hakan bai dace ba ko ya sabawa doka.
A karo na biyu cikin wa'adin mulkinsa na shekaru hudu Majalisar Wakilan Amurka ta sake tsige shugaban kasa Donald Trump. Kuma zai fuskanci shari'a a Majalisar Dattawa bayan sabon shugaban kasa ya fara aiki.
Sabanin yadda a baya aka yi ta muhawara, kan ko shugaban kasa zai iya yafe wa kansa laifi, yanzu abin ya zama muhimmiyar muhawara tun bayan da magoya bayan Trump su ka fusata tare da afkawa ginin Majalisar Dokokin Amurka.
Filin Ciki Da Gaskiya ya fara duba batun korafin jama'a a Kanon dabo, kan yunkurin gwamnatin jihar na raba wasu filaye ko wurare masu muhimmanci ga daidaikun mutane da wasu ke ganin hakan bai dace ba ko ya sabawa doka.
A dai dai lokacin da mataimakin shugaban Amurka Mike Pence, ke jagorantar 'yan Majalisun Amurka biyu a bikin tabbatar da kuri'un kwaleji da zababben shugaban kasa Joe Biden ya samu a zaben Nuwamba, magoya bayan Trump cikin fushi sun afkawa Majalisar tare da dakatar da wannan biki.
A Jamhuriyar Nijar, ana can ana ci gaba da kidaya kuri’ar zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki da aka yi jiya Lahadi yayin da al’umar kasar ta fara dakon sakamakon zabe.
Jiya Talata Hukumar zartarwa ta Tarayyar Turai EU - ta ba da shawarar kasashen EU su dage takunkumin tafiye-tafiye da aka kakaba wa Birtaniyya don kauce wa katse hanyoyin samar da kayayyaki da makalewar matafiya.
Jiya Talata zababben shugaban Amurka Joe Biden ya nuna juyayi ga iyalai masu gwagwarmaya, kuma ya yaba wa Majalisa don zartar da kudirin tallafin coronavirus yayin da kasar ke ci gaba da samun karuwar COVID-19 da ta addabi kowa ana shirin bikin Kirsimeti.
Domin Kari