Shugaban kungiyar Miyatti Allah na jihar Kaduna, Alhaji Haruna Usman Tugga, ya ce harin da aka kai ba na ramuwa ba ne domin Fulani ba su kai wa kowa hari ba.
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari garin Wawan Rafi, gabannin wannan hari da aka kai wa Fulanin garin Kurmin Bi, wanda kungiyar al’ummar Kudancin Kaduna ta SUKAPO ta ce ana zargin Fulani ne, a cewar mai magana da yawun kungiyar Mista Luka Biniyat.
Hare-haren ramuwar gayya na neman zama ruwan dare a wasu sassan Najeriya, amma shugaban kungiyar Miyetti Allah, ya ce suna iyaka kokarinsu wajen ganin an magance faruwar hakan. Duk da yake ya ce akwai wasu da basa son zaman lafiya kuma sun ja kunnen ‘yan kungiyarsu da su rika barin gwamnati ta dauki matakin da ya kamata.
Yawancin lokuta rikice-rikecen kudancin Kaduna kan lafa, amma wani lokaci kuma sai ya dawo, lamarin da Mista Luka ya ce a kowane lokaci suna zama cikin zullumi da kuma shirin ko ta kwana.
Barazanar tsaro na zuwa a daidai lokacin da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Mallam Samuel Aruwan, ke cewa gwamnati na matsa lamba wajen ganin an kama masu hana zaune tsaye da kuma ‘yan ta’adda.
Wannan barazanar tsaro dai na zuwa ne daidai lokacin da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jahar Kaduna, Malam Samuel Aruwan ke cewa gwamnati na matsa lamba don danko masu hana zaune tsaye da kuma 'yan ta'adda.
Saurari rahotan Isah Lawal Ikara a sauti: